Imo: Yadda mayakan IPOB suka kashe direbobin tirelar Dangote 3, suka babbaka gawawwakin su

Imo: Yadda mayakan IPOB suka kashe direbobin tirelar Dangote 3, suka babbaka gawawwakin su

  • Wasu ‘yan ta’adda da ake zargin mayakan IPOB ne sun halaka direban tirelar Dangote, Saidu Alhassan da mataimakan sa, Halliru Mallam da Danjuma Isari a karamar hukumar Orsu da ke jihar Imo
  • Lamarin ya faru ne a ranar Laraba kuma direbobin sun kama hanyar komawa Obajana, jihar Kogi ne bayan sun sauke simintin da su ka kai ma’ajiyar simintin Dangote da ke Orlu
  • Majiyoyi sun bayyana yadda ‘yan ta’addan su ka fara umartar su da su sauka daga motar, bayan sun fahimci cewa duk ‘yan arewa ne sai su ka harbe su har lahira kuma suka kona gawarsu

Imo - Wasu da ake zargin mayakan IPOB ne sun halaka direban tirelar Dangote, Saidu Alhassan da mataimakan sa 2, Halliru Mallam da Danjuma Isari a karamar hukumar Orse da ke jihar Imo.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

Daily Nigerian ta tattaro bayanai akan yadda lamarin ya faru a ranar Laraba yayin da direbobin suke hanyar komawa wurin aikinsu, Obajana da ke jihar Kogi.

Imo: Yadda mayakan IPOB suka kashe direbobin tirelar Dangote 3, suka babbaka gawawwakin su
'Yan IPOB sun kashe direbobin motar Dangote a Imo, sun kona gawarsu. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyi sun bayyana yadda makasan su ka umarce su da su sauka daga motar, bayan sun gane ‘yan arewa ne su ka harbe su har lahira kuma su ka babbaka gawawwakin su, a ruwayar Daily Nigerian.

An tsinci gawawwakin ne a ranar Alhamis kusa da tirelar, daga baya aka dauke su aka mayar da su Obajana.

Tun bayar tashin sabuwar guguwar rashin tsaro a kudu maso gabas, jami’an tsaro, ‘yan arewa da kuma duk masu karya dokar zama a gida su ke fuskantar farmaki daga ‘yan kungiyar IPOB.

Ba wannan ba ne karo na farko

A watan Mayun wannan shekarar, ‘yan ta’addan sun halaka Ahmed Gulak, tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan shawarwari a bangaren siyasa.

Kara karanta wannan

Dalibai sun yo hayar ‘yan daba domin su lallasa malamansu, an jikkata wasu

A watan Afirilu kuma, mayakan IPOB su ka bude wa masu sayar da suya guda 6 wuta a Orlu da kuma wani a Umuaka Njaba.

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A jiya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel