Ministan tsaro da shugabannin tsaro sun dira Borno kan sabbin harin ISWAP

Ministan tsaro da shugabannin tsaro sun dira Borno kan sabbin harin ISWAP

  • Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya tare da hafsoshin sojin kasar nan sun isa garin Maiduguri da ke Borno
  • Ministan tsaron tare da hafsoshin tsaron sun fada ganawar sirri da kwamandan Operations Hadin Kai, CG Musa
  • Wannan na zuwa ne bayan 'yan ta'adda sun kai farmaki garin Damboa inda a take aka rasa rayukan mutum hudu

Borno - Ministan tsaro, manjo janar Bashir Salihu Magashi mai ritaya ya dira Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Bashir ya jagoranci dukkan hafsoshin tsaro tare da manyan sojojin kasar nan domin duba yanayin ayyukan da rundunar sojin kasar nan ke yi a can, Daily Trust ta wallafa.

Ministan tsaro da shugabannin tsaro sun dira Borno kan sabbin harin ISWAP
Ministan tsaro da shugabannin tsaro sun dira Borno kan sabbin harin ISWAP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wadanda ke cikin tawagar sun hada da shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, shugaban sojojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya, shugaban sojin sama, Aisr Marshal Isiaka Amao da shugaban sojin ruwa, Rear Admiral Awwal Gambo.

Kara karanta wannan

Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani

A halin yanzu sun shiga ganawar sirri da shugaban rundunar Operations Hadin Kai, Manjo Janar CG Musa tare da sauran kwamandojinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan lamarin na zuwa ne bayan farmakin da 'yan ta'adda suka kai garin Damboa inda aka rasa rayuka hudu, Daily Trust ta wallafa.

Karin bayani na nan tafe...

Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya da ke aiki da rundunar Operation HADIN KAI sun halaka wasu 'yan ta'adda tare da samo a kalla motocin yaki biyu tare da buhunan taki 622 da suke amfani da shi wurin hada bama-bamai.

An halaka 'yan ta'addan a sassa daban-daban na jihar Borno da suka hada da kauyukan: Dar, Kumshe, Wulgo, Chabbol da Kijmatari duk a jihar Borno da kuma titunan Ngala zuwa Wulgo da Nguru zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da motocci masu bindiga 15 suna can sun kai hari Damboa

Mukaddashin yada labaran tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel