Na kare kai na ne: Matar aure ta kashe mijinta da suka shafe shekara 35 suna zaman aure

Na kare kai na ne: Matar aure ta kashe mijinta da suka shafe shekara 35 suna zaman aure

  • Yan sanda a jihar Rivers sun kama wata matar aure Gladys Amadi bisa zargin halaka mijinta Napoleon Amadi
  • Bayan bincike, Gladys wacce suka shafe shekaru 35 tare da mijinta ta amsa cewa ita ta kashe shi da adda amma kare kai ne
  • Gladys ta ce mijinta ne ya dakko addar da nufin zai halaka ta sannan ya yi tsafi da yaranta biyu amma ta yi galaba a kansa

Rivers - Yan sanda a jihar Rivers, a ranar Alhamis sun ce sun kama wata mata mai shekaru 51, Gladys Amadi, daga Chokocho a karamar hukumar Etche a jihar kan kashe mijinta, Napoleon Amadi, da adda.

Kakakin yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ne ya sanar da hakan yayin holen wacce ake zargin gaban manema labarai a ofishin CID, Port Harcourt, babban birnin jihar, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Mun kammala bincike a kan Abba Kyari - Shugaban ‘Yan Sanda ya fadi abin da ake jira

Na kare kai na ne: Matar aure ta kashe mijinta da suka shafe shekara 35 suna zaman aure
Kare kai ne: Matar aure ta kashe mijinta da suka shafe shekara 35 suna zaman aure. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto Omoni ya ce, an kama Gladys ne a ranar 8 ga watan Oktoban 2021 kuma ta amsa cewa ta aikata laifin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Bincike ne kan kisan wani Napoleon Amadi. Yan sanda sun tashi sun fara bincike.
"Binciken ya yi sanadin kama wata mata da wasu. Bayan zurfafa bincike, ta amsa cewa ita ta kashe mijinta; sun yi rikici ne sai da yamma ya fito da adda zai yanke ta amma ta kwace ta kashe shi da shi.
"Ta sare shi a wuri da dama a goshinsa, hakan ya yi sanadin mutuwarsa."

Kakakin yan sandan ya ce bincike ya nuna Gladys ta wanke jinin bayan halaka mijin don boye abin da ya faru.

Kare kai na na ke yi, yana son kashe ni da yara na don asiri, Gladys

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi

Da ta ke magana da manema labarai, Gladys ta ce kare kanta ta yi, ta kara da cewa mijinta ya yi niyyar kashe ta ne bayan sun samu sabani.

Wanda ake zargin ta ce ta janyo hankalin mutane kan lamarin amma babu wanda ya kula ta.

Ta kuma yi ikirarin cewa mijinta ya yi barazanar kashe ta da yaranta domin yin asiri, ta ce shekarunsu 35 suna zaman aure.

Kakakin yan sandan ya ce za a gurfanar da ita a kotu bayan kammala bincike.

Kotu ta ɗaure malaman addinin musulunci 2 da aka kama da sassan jikin bil’adama a Kwara

A wani rahoton, kotu ta yanke wa malaman addinin musulunci, Olaitan Folorunsho Abdulwahab da mahaifinsa, Suleiman Babatunde, hukuncin zama a gidan yari bisa mallakar sassan jikin bil-adama.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda malamin ya yi amfani da gawar wani Suleiman Saka bayan tono ta daga kabari.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan fashi suka harbi mai shagon POS saboda kin basu kudi cikin dadin rai

Alkalin kotun, Bio Saliu ya yanke wa Abdulwahab shekaru 4 a gidan yari yayin da mahaifin sa zai yi watanni 4 sannan ya biya harajin N3,000 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel