Da duminsa: An bankado farmakin balle gidan gyaran halin Edo

Da duminsa: An bankado farmakin balle gidan gyaran halin Edo

  • Jami'an tsaro a jihar Edo sun bankado wani yunkurin balle gidan fursunan jihar da ke Benin City
  • Kamar yadda mai magana da yawun gidan ya tabbatar, mazauna gidan ne suka tada mummunar zanga-zanga
  • Hargitsin ya fara ne daga wadanda ke jiran hukunci, wadanda aka kamo da kuma wadanda aka yanke wa hukunci

Edo - Jami'an hukumar gyaran gidan gyaran hali, 'yan sanda da rundunar soji a ranar Alhamis sun bankado wani yunkurin balle gidan gyaran halin da mazauna cikinsa suka yi kan babban titin Sapele a Benin City, jihar Edo.

Wasu da ke jiran hukunci, ballantana wadanda aka sake cafkewa, sun balle zanga-zanga a yunkurinsu na tserewa amma jami'an tsaro suka hana su, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Da duminsa: An bankado farmakin balle gidan gyaran halin Edo
Da duminsa: An bankado farmakin balle gidan gyaran halin Edo. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar gidan gyaran halin, Aminu Suleman, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce babu wanda ya tsere kuma babu wanda ya mutu yayin zanga-zangar.

"Yunkurin balle gidan wanda aka fara wurin karfe goma sha biyu da rabi na rana, an fara ne bayan arangamar tsakanin wadanda ke jiran shari'a, ballantana wadanda suka taba guduwa aka cafko su da kuma wadanda aka yanke wa hukunci," yace.

Ya ce wannan cigaban ya kawo hatsaniya tsakaninsu da wadanda aka yanke wa hukunci.

Kamar yadda yace, tuni aka kara jami'an tsaro wadanda aka aiko daga hedkwatar jihar domin tabbatar da doka da oda.

Ya ce a halin yanzu an tabbatar da komawar komai lafiya inda ya kara da cewa ana cigaba da bincike domin gano yadda lamarin ya faru da abinda ya assasa shi.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun saki ‘yan asalin jihar Benue da suka sace a Zamfara

Bayan kwanaki 4 da balle gidan, 'Yan sanda sun cire bam a gidan gyaran halin Oyo

A wani labari na daban, kwanaki hudu bayan 'yan bindiga sun kai farmaki tare da sakin daruruwan jama'a daga gidan gyaran hali da ke Abolongo a jihar Oyo, 'yan sanda sun cire bam a gidan.

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, bam din ya na daga cikin wadanda 'yan ta'adda suka dasa yayin farmakin da suka kai gida a ranar Juma'a da ta gabata.

Yayin da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar gidajen gyaran hali ta jihar, Olanrewaju Anjorin, ya tabbatar da aukuwar lamarin, The Guardian ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel