Da Duminsa: Yar majalisar dokoki ta jam'iyyar PDP ta rigamu gidan gaskiya

Da Duminsa: Yar majalisar dokoki ta jam'iyyar PDP ta rigamu gidan gaskiya

  • Yar majalisar dokokin jihar Cross Ribas, Elizabeth Ironbar, ta riga mu gidan gaskiya bayan fama da rashin lafiya
  • Honorabul Ironbar ta mutu ne ranar Talata 26 ga watan Oktoba, kuma itace yar majalisa ta biyu da ta mutu a majlisa ta 9
  • Kafin rasuwarta, marigayya ta kasance mamba a jam'iyyar hamayya PDP kuma ta ɗare kan mulki tun shekarar 2015

Cross River - Yar majalisar dokokin jihar Cross Ribas na tsawon zango biyu, Hon. (Lady) Elizabeth Edem Ironbar, ta rigamu gidan gaskiya.

Vanguard ta rahoto cewa Honorabul Ironbar, wacce ta wakilci majalisar dokoki ta 8 da kuma ta 9 ta mutu ne da daren ranar Talata 26 ga watan Oktoba, 2021.

Wata majiya daga iyalan marigayiyar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace Elizabeth Ironbar ta mutu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Read also

Babbar Magana: Wani Mutumi ya damfari malamin addini miliyan N1.2m, An gurfanar da shi gaban Kotu

Elizabeth Ironbar
Da Duminsa: Yar majalisar dokoki ta jam'iyyar PDP ta rigamu gidan gaskiya Hoto: Vanguardngr.com
Source: UGC

Yar majalisan ta yi ƙaurin suna a jihar ne saboda kudirinta na kafa hukumar masu naƙasa a jihar.

Shin majalisa tasan da mutuwan?

Da yake tabbatar da mutuwar abokiyar aikinsa, Honorabul Itam Abang, mai wakiltar mazaɓar Boki ta ɗaya, yace:

"Muryar farin cikin mutanen birni, kin yi gwagwarmaya duk rintsi, na jinjina miki Honorabul Elizabeth Ironbar. Mu kwana lafiya abar ƙaunar mu."

Legit.ng Hausa ta gano cewa ita ce yar majalisa ta biyu da ta rasa ranta a majalisar jiha ta 9, bayan Godwin Akwaji, na jam'iyyar PDP, wanda ya mutu a watan Yuni 2020.

Hakanan kuma Ironbar itace yar majalisar dokoki ta huɗu da ta mutu a majalisu biyu tun daga shekarar 2015 zuwa yanzun.

Sauran da suka mutu sun haɗa da, Stephen Ukpukpen (PDP), da kuma Simon Nkoro Egbung (PDP), kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Read also

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Kafin rasuwarta, Honorabul Ironbar ta kasance mamba a jam'iyyar PDP, kuma ta lashe zaɓe kuma ta sake komawa a shekarar 2015 da 2019.

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya zargi yan siyasar ƙasar nan da rura wutar rikici a jiharsa

Lalong yace sunan da ake wa Filato lakabi da shi, shine gidan zaman lafiya da wurin shakatawa, amma yan siyasa sun bata komai.

A cewar gwamnan, takwarorinsa na Arewa suna goyon bayan kirkiran yan sandan jiha domin kawo ƙarshe ƙalubalen tsaro.

Source: Legit

Online view pixel