Gwamnonin Kudu sun bukaci shahararren malami a Najeriya ya daina caccakar Shugaba Buhari

Gwamnonin Kudu sun bukaci shahararren malami a Najeriya ya daina caccakar Shugaba Buhari

  • Gwamnonin kudu maso gabas sun roki Rabaran Ejike Mbaka, ya daina sukar da yake wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • Gwamnonin sun bayyana cewa suna iyakar bakin kokarin su wajen tabbatar da gwamnatin tarayya ta sako Nnamdi Kanu
  • Gwamna Umahi, shugaban ƙungiyar gwamnonin shine ya yi wannan rokon a wurin taron shekara a majami'ar babban malamin

Abuja - Gwamnonin yankin kudu maso gabas sun roki shahararren malamin nan na addinin kirista, Rabaran Ejike Mbaka, ya daina magana mara ɗaɗi akan shugaban ƙasa Buhari.

Shugaban gwamnonin yankin, Gwamna David Umahi, tare da rakiyar gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, na jihar Enugu, sune suka roki malamin amadadin sauran.

Punch ta rahoto cewa gwamnonin sun miƙa wannan bukatar tasu ga malamin ne yayin bikin shekara-shekara na majami'arsa ranar Lahadi.

Shugaba Buhari da Mbaka
Gwamnonin Kudu sun bukaci shahararren malami a Najeriya ya daina caccakar Shugaba Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Muna kokarin ceto Nnamdi Kanu - Gwamnoni

Kara karanta wannan

Wasu gwamnonin Arewa sun bada tallafin miliyan N20m ga iyalan mutanen da aka kashe a Sokoto

Gwamna Umahi ya shaidawa Rabaran Mbaka cewa gwamnonin Kudu-Gabas da sauran manyan mutanen yankin, suna ƙoƙari wajen ganin gwamnati ta saki shugaban yan aware, Nnamdi Kanu, nan bada jimawa ba.

Yayin bikin addu'a a majami'ar ta Mbaka, Gwamna Umahi ya bada tallafin miliyan N30m da kuma doya 200 da buhunan shinkafa 100 ga majami'a.

Meyasa suka yi wannan rokon?

A cewar ƙungiyar gwamnonin ta bakin Umahi, shugaba Buhari yana kokari matuka wajen saita tattalin arzikin kasar nan domin rage raɗaɗin talauci.

Channels tv ta rahoto Gwamnan yace:

"Waɗan da aka zaɓa su rike madafun iko, ya zama haƙƙi akan su samar da kyakkyawan jagoranci da yanayi mai kyau ga mutanen da suka zaɓe su."

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kutsa kai wurin Ibada ana tsaka da bauta, Sun yi awon gaba da mutum 3

Kara karanta wannan

Labari da Hotuna: Kada ka sadaukar da rayuwarka kan yan siyasa, Gwamna ya halarci bikin ɗan babban abokin hamayyarsa

Wasu tsagerun yan bindiga sun kutsa kai cikin wata coci ana tsaka da ibada a Oba Oko, ƙaramar hukumar Ewekoro

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da masu bauta mutum uku kuma sun nemi miliyoyin kuɗin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel