Da dumi: Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin e-Naira tare da Gwamnan CBN

Da dumi: Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin e-Naira tare da Gwamnan CBN

  • eNaira wani sabon kudin Najeriya ne da Bankin CBN zai fitar don amfanin yan Najeriya
  • CBN yayi bayanin yadda yan Najeriya zasu iya amfani da wannan Naira kan wayoyinsu
  • Bayan kaddamar da kudin, shugaban kasan ya tafi Amurka

FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da kudin intanet na Najeriya, e-Naira, ranar Litinin, 25 ga Oktoba, a fadar Aso Villa dake birnin tarayya Abuja.

Wadanda ke hallare a taron kaddamar da kudin sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Gwamnan bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.

Da dumi: Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin e-Naira tare Gwamnan CBN
Da dumi: Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin e-Naira tare Gwamnan CBN Hoto: Bashir Ahmed
Source: Facebook

Abubuwan da ya kamata ku sani game da kudin intanet na Najeriya

CBDC wakilci ne na tsarin kudaden intanet masu cikakken iko da ake samar da su kamar yadda Babban Banki ke samar da kudi gama-gari.

Read also

Dama ta samu: Buhari zai ba masu digiri bashin miliyoyi saboda rage zaman banza

Alhakin kai tsaye ne na Babban Banki ke samar dashi. Ba ana nufin maye gurbin tsabar kudi da tsarin ajiyar banki bane, ana nufin su yi aiki kunnen doki a matsayin karin nau'in hanyar biyan kudi da karba.

Ta yaya CBDC zai gudana?

CBN ya yi bayanin cewa tsarin eNaira CBDC ya hada da matakai 4 zuwa cikakken aiwatarwa da kuma tafiyarwa.

CBN ne ke da alhakin kerawa, kirkira da adana CBDC.

Za a rarraba CBDC ga cibiyoyin kudi da masu hada-hadar kudi masu lasisi wadanda za su ba da su ga mutane da sauran kasuwanni.

Cinikayya da CBDC na iya kasancewa akan yanar gizo ko akasin haka. Mutane da kamfanoni za su iya huldar kasuwa dashi nan take ta hanyar tashoshin biyan kudi na yanzu da na nan gaba (misali wayar hannu).

Read also

Shugaba Buhari zai kaddamar da e-Naira ranar Litinin kafin ya tafi Saudiyya

CBN za ta ci gaba da sa ido da kula da CBDC.

Source: Legit

Online view pixel