Sunaye: Jihohi 33 na Najeriya da za su kasa biyan albashin ma'aikata saboda rashin tallafin FG
- Akwai yuwuwar wasu jihohi 33 na Najeriya su kasa biyan albashi saboda gwamnatin tarayya ba za ta iya ba su kaso daga kudin shiga ba
- Gwamnatin tarayyar za ta yi amfani da kudi har N172 billion ga mashawarta masu zaman kansu kan Paris Club refund
- Jihohi uku ne kacal a fadin kasar nan za su iya dogaro da kansu wurin aiwatar da ayyukan yau da kullum ba tare da daukin FG ba
Wasu jihohi 33 na kasar nan zai yuwu su gaza biyan albashi bayan hukuncin gwamnatin tarayya na diban wasu kdui daga asusun kananan hukumomi domin biyan wasu mashawarta masu zaman kansu kan Paris Club refund
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, BudgIT, wata kungiya mai zaman kanta a rahotoon da ta fitar, ta ce jihohi 3 kacal ne a Najeriya za su iya daukan nauyin ayyukan yau da kullum din su ba tare da dogara da tallafin gwamnatin tarayya ba.
Jihohin da za su iya kasa biyan ma'aikata sun hada da:
Adamawa
Anambra
Bauchi
Bayelsa
Benue
Borno
Cross River
Delta
Ebonyi
Ekiti
Enugu
Gombe
Jigawa
Kaduna
Kano
Katsina
Kebbi
Kogi
Kwara
Nasarawa
Niger
Ogun
Ondo
Osun
Oyo
Plateau
Sokoto
Taraba
Yobe
Zamfara
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta dinga uzzura wa tare da kokarin hana gwamnatin tarayya biyan makuden kudi har $418 million (N172 billion) ga mashawartan
Sai dai a wani juyi da gwamnatin tarayyar ta yi kasa da wata daya bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ma'aikatar kudi, kasafi da tsari ta fara zabtare kudaden domin biyan mashawartan.
Babban sakataren mai'aikatar kudi, ya sanar da kwamitin kula da asusun gwamnatin tarayya, FAAC, a taron da suka yi ranar Juma'a cewa sun fara zabtarar kudin domin biyan mashawartan, Daily Trust ta ruwaito.
Yan IPOB sun kai hari ofishohin yan sanda 164, sun kashe jami'ai 175, duka laifin Nnamdi Kanu ne: FG
Biyan kudin Paris Club
A 2006, gwamnatin tarayya ta biya $12 biliyan domin samun yafiyar bashin $18 biliyan daga Paris Club.
Wasu mashawarta sun bayyana inda suke ikirarin cewa akwai wani kaso na kudin da aka yi za a biya su kan aikinsu ga gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi.
An bukaci ALGON da su yi wasu 'yan kwangilar da wasu manyan ayyuka a fadin kasar nan.
Sai dai kuma an dinga tambayoyi kan dalili da zai sa a bukaci mashawarta domin sasanci tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya, bayan kuma kwangilar da aka bai wa ALGON ta bi shanun sarki.
Asali: Legit.ng