Tirkashi: Kansiloli suna zargin shugaban ƙaramar hukuma da 'satar' injin janareta

Tirkashi: Kansiloli suna zargin shugaban ƙaramar hukuma da 'satar' injin janareta

  • Kansiloli a karamar hukumar Mkpat Enin sun zargi shugaban karamar hukumar da satar janareta
  • A cikin korafin da suka aike wa majalisar dokokin jihar sun kuma zarge shi da bannatar da kudade
  • Mr Ekpo, shugaban karamar hukumar Mkpat Enin ya ce a bashi lokaci domin ya yi nazarin zargin da ake masa

Akwa Ibom - Wasu kansiloli a jihar Akwa Ibom sunyi zargin shugaban karamar hukumarsu ya hada baki mutane domin 'gwanjon' wani babban janareta na karamar hukumar.

Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom ta fara bincike kan zargin da ake yi wa shugaban karamar hukumar na Enin, Aniekpon Ekpo, bayan 10 cikin 14 na kansilolin sun saka hannu a takardan korafi.

Bisa ga ruwayar Premium Times, baya ga sata, kansilolin sun kuma zargi Mr Ekpo da bannatar da kudade da amfani da karfin ofishinsa ta hanyoyin da basu dace ba.

Read also

Dakarun sojoji sun yi arangama da matasa a Imo, an ƙone gidaje da dama

Tirkashi: Kansiloli suna zargin shugaban ƙaramar hukuma da 'satar' injin janareta
Mr Aniekpon Ekpo, shugaban karamar hukumar Mkpat Enin a jihar Akwa Ibom. Hoto: Premium Times
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin takardar korafin da kansilolin suka tura wa kakakin majalisar dokokin jihar, Aniekan Bassey, sun nemi a dakatar da shugaban karamar hukumar har sai an gama bincike.

Sun ce:

"Cikin sirri, shugaban karamar hukumar ya yi gwanjon wani janareta mara-kara mallakar karamar hukumar batare da sanarwa ba ko bin ka'ida.
"Ana iya fassara abin da ya aikata a matsayin sace kayan karamar hukuma."

Kansilolin sun ce wasu matasa a yankin sun hana wani babban mota daukan babban janaretan don tafiya da shi.

An zabi Mr Ekpo a matsayin shugaban karamar hukumar Mkpat Enin ne a watan Disamban 2020 karkashin jam'iyyar PDP.

Kansilolin sun ce tunda aka zabe shi bai taba bada ba'asi ba game da harajin da ya ke karba duk wata.

Martanin Mr Ekpo

Da Premium Times ta tuntubi shugaban karamar hukumar, ya ce bai riga ya samu cikaken bayani kan korafin da aka shigar a kansa ba.

Read also

Muhyi: Kotu ta bukaci ganin kakakin majalisar jihar Kano da wasu mutane 5

"Ban riga na samu cikaken bayani game da korafin ba, zan mayar da martani daga baya," - Mr Ekpo

Majalisar dokokin Akwa Ibom ta fara bincike

Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom ta fara zaman sauraron korafe-korafen da kansilolin suka shigar.

Mark Esset, shugaban kwamitin kananan hukumomi da masarautu, ya tabbatar da hakan cikin sanarwa da ya fitar.

Yayin zaman na farko a ranar 18 ga watan Okotoba, dukkanin kansilolin da suka rattaba hannu kan takardan sun sake jadada korafinsu a gaban kwamitin.

Amma an samu tangarda yayin zaman domin Mr Ekpo ya yi ikirarin ba a bashi kwafin takardar korafin ba.

Daga bisani an bashi kwafin takardan korafin, kuma kwamitin ta umurci ya bada amsa kafin 20 ga watan Oktoba, yayin da aka dage cigaba da zaman zuwa ranar 22 ga watan Oktoba.

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari.

Read also

Kasafin kudin Buhari: Za a sayi janareta na N104bn, aikin wutar Mambila kuma N650m

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel