Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000

Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000

Ibadan - Akalla fursunoni dubu daya sun gudu daga gidan gyara halin Abolongo a garin Oyo bayan harin da wasu yan bindiga suka kai suka saki dukkan wadanda ke tsare a wajen.

TVC ta ruwaito cewa yan bindigan sun dira gidan yarin ne misalin karfe 11 na dare kuma suka budewa jami'an tsaro wuta.

Ga hotuna yadda yan bindiga suka yi da wajen:

Yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000
Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000 Hoto: tvcnewsng
Asali: Facebook

Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000
Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000 Hoto: tvcnewsng
Asali: Facebook

Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000
Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000 Hoto: tvcnewsng
Asali: Facebook

Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000
Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000 Hoto: tvcnewsng
Asali: Facebook

Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000
Hotunan yadda yan bindiga suka fasa gidan yari suka saki Fursunoni 1000 Hoto: tvcnewsng
Asali: Facebook

Hukumar gidajen gyara hali ta jihar Oyo, ta bayyana cewa Fursunoni 837 ne suka arce daga gidan yarin Abolongo sakamakon harin da yan bindiga suka kai daren Juma'a.

Kara karanta wannan

Harin Oyo: Hukumar Gidajen Yari ta bayyana adadin Fursunonin da suka gudu da wadanda aka damko

Kakakin hukumar, Olanrewaju Anjorin, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, a Ibadan, rahoton NAN.

Olanrewaju yace dukkan Fursunonin dake sauraron gurfana gaban kotu 837 ne suka arce amma wadanda tuni aka yanke musu hukunci na nan ba'a shiga inda aka ajiyesu ba.

Yace kawo yanzu an damko mutum 262 cikin wadanda suka gudu, yayinda ake neman 575.

Mun kawo muku rahoton cewa yan bindiga sun kai hari gidan yarin dake Abolongo, a jihar Oyo ranar Jumu'a da daddare.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin gidan yarin, sannan suka saki dukkan fursunonin dake ciki.

Miyagun yan bindigan sun fasa gidan yari ne da tsakar dare, inda suka yi amfani da gurneti wajen tilasta samun damar shiga harabar gidan gyaran halin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel