Majalisa za ta mika ƙudurin ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda gaban fadar shugaban kasa

Majalisa za ta mika ƙudurin ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda gaban fadar shugaban kasa

  • Majalisar dattawa za ta mika kudiri ga shugaban kasa Buhari kan ya ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda
  • 'Yan majalisar sun bukaci shugaban kasa da ya bai wa sojoji damar murkushe maboyarsu tare da ganin bayansu
  • Majalisar wakilan Najeriya ta goyi bayan hakan inda ta ce hakan ne zai sa hukuncin ya shafi har da masu daukar nauyinsu

FCT, Abuja - A ranar Alhamis, majalisar dattawa ta ce mako mai zuwa za ta mika kudiri ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda.

Daily Trust ta wallafa cewa, majalisar za ta mika kudirin ne ta hannun sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Mustafa Boss.

A ranar 29 ga watan Satumba, majalisar dattawan ta mika kudiri gaban Buhari kan ya ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda kuma ya saka kafar yaki da su.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa

Majalisa za ta mika ƙudurin alanta 'yan bindiga da 'yan ta'adda gaban fadar shugaban kasa
Majalisa za ta mika ƙudurin alanta 'yan bindiga da 'yan ta'adda gaban fadar shugaban kasa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sun sake da bukatar shugaban kasa da ya bai wa dakarun sojin kasar nan da su karar da su ta hanyar ragargaza maboyarsu.

Wannan kudirin ya biyo bayan wata bukata da Sanata Ibrahim Gobir daga Sokoto ya mika inda ya jajanta cewa yankin Sokoto ta gabas yanzu ta zama wurin zaman 'yan bindiga bayan fatattakarsu da ake yi daga Zamfara.

Washegarin ranar, majalisar wakilai ta sake mika wannan kudirin bayan wata bukata da Babajimi Benson daga Legas ya mika.

Benson wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro, ya ce ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda zai sa a hanzarta kaddamar musu da hukunci a karkashin dokokin ta'addanci na 2011.

"Wannan umarnin zai kawo karshen al'amuran 'yan ta'adda da masu daukar nauyinsu karkashin dokar hana ta'addanci. Kuma duk wanda aka kama ya na da alaka da kungiyoyin za a iya gurfanar da su tare da yanke musu hukunci," yace.

Kara karanta wannan

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

A yayin martani ga Daily Trust kan halin da ake ciki, daraktan yada labarai na majalisar dattawa, Rawlings Agada ya ce, "Kokarin mika kudirin za mu iya cewa ya kai matakin karshe a wurin magatakardan majalisar kuma za a mika ofishin SGF."

El-Rufai ya rubuta wasika, yana so a ayyana ‘Yan bindigan Arewa a matsayin ‘yan ta’adda

A wani labari na daban, Malam Nasir El-Rufai ya yi kira ga gwamnati ta ayyana miyagun ‘yan bindigan da suka addabi Arewa maso yammacin kasar nan a matsayin ‘yan ta’adda.

Jaridar Daily Trust ta rahoto gwamnan jihar Kaduna yana so a jefa wadannan ‘yan bindagan a rukunin ‘yan ta’adda ko kuma masu tada kayar baya a Najeriya.

Gwamnan ya bayyana cewa yin hakan zai taimaka sojojin Najeriya su hallaka duk wani ‘dan bindiga da aka kama, ba tare da jawo fushin kasan Duniya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel