Bayan kwanaki da halaka Al-Barnawi, sojin Najeriya sun sheke magajinsa, Malam Bako

Bayan kwanaki da halaka Al-Barnawi, sojin Najeriya sun sheke magajinsa, Malam Bako

  • Dakarun sojin Najeriya sun sheke Malam Bako, shugaban ISWAP da ya gaji Abu Mus'ab Al-Barnawi
  • NSA Munguno ya ce babu shakka sojin Najeriya sun nakasa ISWAP ganin cewa cikin wata 1 aka halaka shugabanninsu 2
  • Munguno ya tabbatar da cewa yanzu haka kungiyar na fama da rikicin shugabanci, yarda, zargi da sauransu

FCT, Abuja - Mai bada shawara ga shugaban kasa kan tsaron kasa, Babagana Munguno, ya sanar da kisan Malam Bako, shugaban ISWAP na yanzu wanda ya gaji Abu Mus'ab Al-Barnawi, TheCable ta wallafa.

Munguno, manjo janar mai ritaya, ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati kan ganawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da shugabannin tsaro a Abuja ranar Alhamis.

Bayan kwanaki da halaka Al-Barnawi, sojin Najeriya sun sheke magajinsa, Malam Bako
Bayan kwanaki da halaka Al-Barnawi, sojin Najeriya sun sheke magajinsa, Malam Bako. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamfanin Dillancin Najeriya ya ruwaito cewa, shugaban ma'aikatan tsaro, CDS, Janar Lucky Irabor ya tabbatar da mutuwar Al-Barnawi a ranar 14 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Farashin Shayi 'Empty' ya tashi a jihar Kano, Kakaakin Masu Shayi

Irabor ya ce: "Zan iya tabbatar muku da cewa Abu Mus'ab ya sheka lahira. Ya mutu kuma bashi da rai."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Alhamis, NSA ya bayyana cewa magajin Al-Barnawi, Malam Bako ya sheka lahira tare da wasu jiga-jigan kungiyar ta'addancin, Daily Nigerian ta wallafa.

Ya ce: "Bayanin cewa, dakarun sojin Najeriya sun yi aiki mai kyau saboda a cikin wata daya an hambarar da shugabancin ISWAP inda aka halaka Al-Barnawi.
"Kwanaki biyu da suka gabata, wanda ya gaje shi, Malam Bako, daya daga cikin fitaccen 'yan majalisar Shura na kungiyar ya sheka lahira.
"A halin yanzu suna fama da rikicin shugabanci. Kun san wadannan abubuwan su kan zo da matsalolin yarda, fada, zargi da sauransu.
"Toh gaskiya ayyukan dakarun sojin kasar nan a arewacin kasar nan ya matsantawa kungiyar Boko Haram da sauran ire-iren kungiyoyinsu na Sahara."

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun nemi jam'iyyun siyasa su ba Tinubu tikitin shugabanci a 2023

Sojin Najeriya sun sheke 'yan ISWAP 16 a Jere, sun kwace motocin yaki

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya a ranar Litinin sun sheke a kalla mayakan ta'addanci na ISWAP 16 a karamar hukumar Jere ta jihar Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa dakarun sojin sun sheke 'yan ta'addan yayin da suke kokarin kaddamar da farmaki a yankin Chabbal da ke wuraren Jere.

'Yan ta'addan sun shiga garin ta yankin Mafa a motocin yaki a yammacin ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel