Sojin Najeriya sun sheke 'yan ISWAP 16 a Jere, sun kwace motocin yaki

Sojin Najeriya sun sheke 'yan ISWAP 16 a Jere, sun kwace motocin yaki

  • Zakakuran sojin Najeriya sun halaka a kalla 'yan ta'addan ISWAP 16 a karamar hukumar Jere ta jihar Borno
  • Mayakan ta'addanci sun yi kokarin kai farmaki yankin Chabbal da ke kusa da jere inda suka shiga garin ta Mafa
  • Dakarun sojin sun dira kan 'yan ta'addan inda suka ragargaza su tare da kwace motocin yakin 'yan ta'addan

Jere, Borno - Dakarun sojin Najeriya a ranar Litinin sun sheke a kalla mayakan ta'addanci na ISWAP 16 a karamar hukumar Jere ta jihar Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa dakarun sojin sun sheke 'yan ta'addan yayin da suke kokarin kaddamar da farmaki a yankin Chabbal da ke wuraren Jere.

'Yan ta'addan sun shiga garin ta yankin Mafa a motocin yaki a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

Sojin Najeriya sun sheke 'yan ISWAP 18 a Jere, sun kwace motocin yaki
Sojin Najeriya sun sheke 'yan ISWAP 18 a Jere, sun kwace motocin yaki. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Mayakan ISWAP din sun fara harbe-harbe babu kakkautawa bayan sun kutsa cikin garin.

Daya daga cikin majiyoyin, wanda jami'in tsaro ne ya sanar da PRNigeria cewa dakarun bataliya 212 da na bataliya ta 195 da ke Jere sun gaggauta daukan mataki inda suka sheke 'yan ta'addan goma sha shida.

Majiyar ta ce:

"'Yan ta'addan sun yi kokarin shiga yankin ta Chabbal domin kai farmaki amma sai zakakuran sojin Najeriya suka dakile su.
"A gaggauce dakarun sojin suka hanzarta tashi tsaye bayan samun bayanan 'yan ta'addan sun shigo. 'Yan ta'addan sun iso a motocin yaki amma sai dakarun suka dakile farmakin tare da kwace wasu daga cikin motocin yakin".

An sheke kwamandojin ISWAP 3, Yaya Ebraheem, Baba Chattimari, Abu Oubaida da wasu 21

A wani labari na daban, a kalla mayakan ta'addancin 24 na ISWAP da suka hada da manyan kwamandoji aka kashe yayin da suka yi kokarin kai wa tawagar rundunar soja hari a Ngamdu, da yammacin Laraba.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan ta'adda da shugabannin 'yan bindiga 12 da aka sheke a 2021

PRNigeria ta tattaro cewa, daga cikin manyan kwamandojin da aka halaka akwai Yaya Ebraheem, Baba Chattimari da Abu Adam Oubaida.

Har ila yau, mataimakin Jaysh na ISWAP a Sambisa, Modou Bacheer Oukocha, ya na daga cikin wadanda suka samu miyagun raunika.

Wata majiyar tsaro daga cikin rundunar ta sanar da PRNigeria cewa, yayin da dakarun sojin kasa suka fara artabu da 'yan ta'addan, jiragen yakin rundunar sojin sama sun isa wurin inda suka fara sakin bama-bamai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel