Jami'an yan sanda sun damke matasan da suka lakadawa Mai SaharaReporter duka yau

Jami'an yan sanda sun damke matasan da suka lakadawa Mai SaharaReporter duka yau

  • Ba tare da tanka musu ba, wasu matasa sun dira kan Omoyele Sowore
  • Sowore wanda tsohon dan takaran kujeran shugaban kasa ne ya halarci taron gurfanar da Nnamdi Kanu ranar Alhamis
  • Wannan ba shine karo na farko da ake kaiwa dan jaridan hari ba

Abuja - Bayan karar da yan jarida suka kai, Jami'an yan sanda sun damke matasan da suka yiwa mai kamfanin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ribiti.

Da farko jami'an tsaro sun yi shiru kan abin da ke faruwa. Yan daban bayan sun daki Sowore sun tafi ba tare da jami’an tsaro sun musu komai ba.

Daga baya yan jarida suka tsawatar kan hakan sannan yan sanda suka damke wasu matasa biyu, rahoton TheCable.

Jami'an yan sanda sun damke matasan da suka lakadawa Mai SaharaReporter duka yau
Jami'an yan sanda sun damke matasan da suka lakadawa Mai SaharaReporter duka yau Hoto: TheCable
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa

Yadda mai SaharaReporters ya sha duka a hannun 'yan daba a harabar kotun Abuja

Yan daba ne sun kai hari ga mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore a babban kotun tarayya da ke Abuja ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba.

Jami’an tsaro sun hana Sowore shiga kotun. Amma yayin da yake magana da jami'an tsaro, wasu yara maza kimanin 20, an lura sun iso wurin, The Nation ta ruwaito.

An lura da kasancewar su a cikin rudani saboda sun yi kama da 'yan neman rikici.

Nan da nan wadanda ake zargin 'yan daban ne suka sauka kan Sowore, suka mare shi tare da kumsa mashi naushi.

Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa

Daga karshe, Jami'an tsaron farin kaya, DSS su sake iza keyar Nnamdi Kanu, shugaban 'yan awaren IPOB zuwa ma'adanarsu.

An gurfanar da Nnamdi Kanu a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargi bakwai da gwamnatin tarayya ke masa a ranar Alhamis, Daily Trust at ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan kimanin kwanaki 120, Dogo Giɗe ya sako ɗaliban Yauri 28 da malamansu biyu da ke hannunsa

Kamar yadda TheCable ta wallafa, Kanu ya musanta zargin da ake masa da suka hada da cin amanar kasa da kuma ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel