An hango sarauniyar kyau ɗare-ɗare bisa acaɓa, bayan cika bakin ba zata iya soyayya da mara mota ba

An hango sarauniyar kyau ɗare-ɗare bisa acaɓa, bayan cika bakin ba zata iya soyayya da mara mota ba

  • Wata sarauniyar kyau ‘yar kasar Uganda ta sha caccaka daga mutane daban-daban a kafafen sada zumuntar zamani
  • Hakan ya biyo wata tattaunawa da wani gidan rediyo su ka yi da ita inda ta ce ba za ta iya soyayya da saurayi mara mota ba
  • Bayan barin gidan rediyon ne aka hango ta dare-dare bisa babur, inda wasu su ka fara cewa ya kamata ta fara mallakar mota kafin ta yi feleke

Uganda - Wata matashiyar budurwa ‘yar kasar Uganda, Doreen Kabareebe ta sha caccaka tun bayan an hango ta bisa babur.

Budurwar a wata tattaunawa da wani gidan rediyo suka yi da ita ta ce ba zata iya soyayya da saurayi mara mota ba a ruwayar Yabaleft.

Bayan wannan furucin ne ta tsayar da babur lokacin da za ta bar gidan rediyon wanda hakan ya sa mutane da dama su ka fara caccakar ta.

Read also

Kallo ya koma sama: Bidiyon ango ɗan Nigeria sanye da siket yana tiƙa rawa a ranar aurensa ya ɗauki hankula

An hango 'babban yarinya' ɗare-ɗare bisa acaɓa, bayan cika bakin ba zata iya soyayya da mara mota ba
An hango ta ɗare-ɗare bisa acaɓa, bayan cika bakin ba zata iya soyayya da mara mota ba. Photo credit: @doreenkabareebe
Source: Instagram

Akwai mutanen da su ka dinga cewa ya kamata ace ta fara siya wa kan ta mota kafin ta yi feleken cewa sai mai mota za ta saurara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Doreen dama sarauniyar kyau ce kuma mai tallar suturu, yayin da ake hirar da ita ta ce ko sauraron namiji ba za ta yi ba idan ba shi da mota, bisa rahoton Yabaleft.

An hango shigar da ta yi yayin hirar da aka yi da ita, iri daya da sanda take bisa babur

Alamu sun nuna cewa ana gama tattaunawar da ita ta hau babur din, tunda an hango rigar, kitson har da agogon da ta yi amfani da su wurin tattaunawar a jikin ta lokacin ta na babur.

Kuma da ma ta wallafa hotunan da ta dauka wurin tattaunawar a shafin ta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

Read also

Yadda jami'an tsaro suka yi wa likita da majinyata lugude a asibitin Abuja

Wasu daga cikin tsokacin da mutane suka yi a kanta

Cikin wadanda su ka caccaketa akwai Velile Noah inda ya ce:

“Ya kamata ta fara siya wa kan ta mota ba wai ta tsaya ta na jiran arzikin wasu ba.”

Congolese Prince ya ce:

“Tana son namiji mai mota amma ba ta da motar, shirmen banza.”

Stephan Ng’andwe ya rubuta:

“Ta na sa sharuddan da ita kan ta ba ta cika ba.”

Hotunan tsohon gwamna ya ɗare kan acaba don gudun kada jirgi ya tashi babu shi a Legas

Tunda farko kun ji cewa bayyanar hotunan tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose dare-dare a kan babur ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

Kamar yadda tsohon gwamnan ya wallafa hotunan a shafin sa na Facebook, sai da ya sauka daga motar sa ne sannan ya dare kan babur a Legas saboda tsabar cunkoso a titin.

Read also

Maryam Booth ta sa an kwamushe matashin da ya yada labarin ta na neman miji

Tsohon gwamnan jihar Ekitin ya yi gudun jirgin su ya tashi ya sa ya yi gaggawar neman babur din don ya samu ya isa filin jirgi cikin hanzari.

Source: Legit.ng

Online view pixel