Maryam Booth ta sa an kwamushe matashin da ya yada labarin ta na neman miji

Maryam Booth ta sa an kwamushe matashin da ya yada labarin ta na neman miji

  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Maryam Booth ta sa an yi mata ram da matashin da ya yi mata kage
  • A kwanakin baya dai an dinga yada cewa jarumar ta koka da yadda aka daina saka ta fim kuma ta na neman miji ido rufe
  • Jarumar ta sha alwashin daukan matakin shari'a kan duk wanda ta sake kamawa da yi mata kage

Shahararriyar jarumar Kannywood, Maryam Booth, ta sa an cafke mata wani matashi da ta zarga da yada labarai na karya kan ta inda aka sa shi yin bidiyo domin neman afuwar ta da janye miyagun kalamansa.

A kwanakin baya, labarin cewa Maryam Booth ta koka da yadda ba a saka ta fina-finai tun bayan bayyana bidiyon tsiraicin ta ya bazu.

Kara karanta wannan

Pandora: EFCC ta yi wa Peter Obi kiran gaggawa kan kamfanoninsa na ketare

Maryam Booth ta sa an kwamushe matashin da ya yada labarin ta na neman miji
Maryam Booth ta sa an kwamushe matashin da ya yada labarin ta na neman miji. Hoto daga @officialmaryambooth
Asali: Instagram

Kamar yadda kagaggen labarin ya bayyana, jarumar ta shiga damuwa kuma ta ce ta na neman miji ido rufe domin ta yi aure ta huta.

Babu shakka labarin ya karade kafafen sada zumuntar zamani inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa da maganganu marasa dadi a kan jarumar.

A cikin makon nan kuwa jarumar ta wallafa wani dogon rubuta na jan kunne da kakkausar murya tare da bidiyon wani matashi da ta bayyana cewa shi ya yada labarin karya a kan ta.

Ta ce daga yanzu duk wanda ya yi mata irin wannan karairayin, ko mahaifiyar da dan uwan ta, to babu shakka za ta dauka mataki a kai.

Kamar yadda ta wallafa a shafin ta na Instagram:

"Kwanaki wata jita-jita ta dinga yawo a kan cewa na tattauna da yaron nan ina neman mijin aure na rasa da sauran miyagun abubuwa dangane da ni.

Kara karanta wannan

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

"Toh duk karya ce kuma wannan yaron ne ya shirya. Zan so in ja kunnen wadannan bata-garin 'yan jaridan balle wadanda ke yanar gizo ballantana na YouTube.
"Daga yanzu zan dauka matakin shari'a kan duk wata kafa da ta wallafa labari a kaina ko 'yan uwana ba tare da tabbatarwa daga wuri na ba.
"Ba zan iya jure ganin mutanen da suka mayar da hankali wurin bata mana suna ba ballantana marigayiyar mahaifiyata. Daga karshe bayan an kama mutum sai ka ji ana cewa "ka yi hakuri ka fi karfin hakan".
"Amma ba za su tuna hakan ba lokacin da suke mugun abu. Na yadda shuhura ta na zuwa da abubuwa da yawa, sai dai kuma barna ma haka. Nagode."

Amma kuma a bidiyon da jarumar ta wallafa na yaron, ya ce shafin Rariya ne suka wallafa labarin, shi kuwa ya yi tsokaci mara dadi a kasan labarin amma ya na neman afuwarta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Dubai ta gwangwaje Jaruma Saratu Daso da kyautar dalleliyar sabuwar mota

Asali: Legit.ng

Online view pixel