Labari Cikin Hotuna: Hukumar NRC ta dakatar da zirga-zirgan jiragen ƙasa a Najeriya

Labari Cikin Hotuna: Hukumar NRC ta dakatar da zirga-zirgan jiragen ƙasa a Najeriya

  • Hukumar NRC ta ƙasa, ta sanar da dakatar da zirga-zirgan jiragen ƙasa a faɗin Najeriya saboda matsalar tsaro
  • Rahotanni sun bayyana cewa wannan matakin na zuwa ne bayan mahara sun kaiwa jirgin Kaduna-Abuja hari har sau biyu
  • Tsohon Sanatan Kaduna da tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana yadda suka samu nasarar tsira bayan jirgin ya taka Nakiya

Abuja - Hukumar sufurin jiragen ƙasa a Najeriya (NRC) ta dakatar da zirga-zirgan jiragen ƙasa a faɗin Najeriya saboda barazanar tsaro.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, Hukumar NRC ta sanar da haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan wasu miyagu sun kai wa jiragen ƙasa dake aiki daga Kaduna zuwa Abuja hari har sau biyu.

Jirgin ƙasa
Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da zirga-zirgan jiragen ƙasa a Najeriya Hoto: NRC FB fage
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kaiwa jirgin dake kan hanyar zuwa Kaduna bayan tsowarsa daga Abuja hari.

Kara karanta wannan

Muna cikin tafiya sai muka ji kara - Fasinjojin jirgin da aka kai wa hari sun bayyana halin da suka shiga

Hakazalika an sake kai farmaki kan jirgin ƙasa karo na biyu, wanda ya taso daga Abuja, ya nufi Kaduna yau Alhamis da safe.

Shin ya fasinjojin cikin jirgin suka yi?

Wasu daga cikin fasinjojin cikin jirgin, waɗanda harin ya ritsa da su, sun bayyana cewa farmakin ya yi sanadiyyar lalacewar layin dogo da jirgin ya saba bi.

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, wanda yana ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin, yace:

"Ranar Alhamis da safe an kaiwa jirgin ƙasa hari, da yammacin Laraba jirgin ya taka bam, kuma an buɗe wa jirgin wuta a saitin direba da kuma tankin mai."
"Ina cikin jirgin da safiyar Alhamis ɗin nan lokacin da jirgin mu ya taka nakiya kuma ta tashi, ikon Allah ne ya tseratar da mu."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun saka Bam a layin dogon Abuja/Kaduna, Shehu Sani ya tsallake rijiya da baya

Hotunan harin da aka kaiwa jirgin ƙasa yau da safe

Harin jirgin ƙasa
Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da zirga-zirgan jiragen ƙasa a Najeriya Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Harin jirgin ƙasa
Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da zirga-zirgan jiragen ƙasa a Najeriya Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Shugaban tashar jirgin ƙasa ta Abuja/Kaduna, Paschal Nnorli, ya tabbatarwa wakilin jaridar Punch cewa an kaiwa jirginsu hari, amma yace bai san da lamarin nakiya ba.

"Eh, an kai wa jirgi hari, amma a halin yanzu ba zan iya tabbatar da cewa harin bam ne ba kamar yadda mutane ke yaɗawa."
"Ana cigaba da bincike, kuma mun tura injiniyoyin mu wurin, duk ƙarin bayanin da muka samu zamu sanar, amma a yanzu an dakatar da zirga-zirga."

A wani labarin kuma Sarkin Musulmi ya roki dakarun tsaro su tasgi tsaye kada du bari wasu bara gurbi su kwace iko da Najeriya

Alhaji Sa'ad Abubakar, yace jahilai masu tsattsauran ra'ayin addini, suke jawo duk rikicin dake faruwa a faɗin Najeriya

Basaraken ya yi wannan furucin ne a wurin taron ilimi na ƙasa na rundunar sojin ƙasa da ya gudana a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel