'Yan bindiga sun saka Bam a layin dogon Abuja/Kaduna, Shehu Sani ya tsallake rijiya da baya

'Yan bindiga sun saka Bam a layin dogon Abuja/Kaduna, Shehu Sani ya tsallake rijiya da baya

  • Sanata Shehu Sani ya sha da kyar bayan 'yan bindiga sun kai hari hanyar jirgin kasa yayin da yake cikin jirgin
  • Tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, ya ce maharan sun dasa bam ne a kan hanyar jirgin, inda ya ce Allah ne kawai ya tsare su
  • Ya yi kira ga dakatar da ayyukan jiragen kasa na Kaduna zuwa Abuja har zuwa lokacin da za a magance lamarin

Kaduna - Tsohon sanata da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya tsallake rijiya da bayan wasu ‘yan bindiga sun far masu a hanyar jirgin kasa.

Shehu Sani wanda ya bayyana halin da ya tsinci kansa a ciki a shafinsa na Facebook, ya ce ya shiga jirgin kasa a safiyar yau Alhamis, 21 ga watan Oktoba, sai kawai jirgin nasu yayi karo da wani abun fashewa da ‘yan bindigar suka dasa a kan hanya.

Read also

Rikicin Shugabancin APC a Kano: Shekarau ya bayyana matakin shi da magoya bayansa suka ɗauka

'Yan bindiga sun hari hanyar jirgin kasa, Shehu Sani ya sha da kyar
Jirgin da aka kai ma hari Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

Sani ya ce ta kai har jirgin ya kusan sauka daga layinsa, ba don Allah ya takaita lamarin ba.

Ya kuma bayyana cewa wannan ba shine karo na farko da irin hakan ke faruwa ba domin a cewarsa, a jiya Laraba, ‘yan bindigan sun kai hari kan wani jirgin Kaduna zuwa Abuja.

Ya ce sun dasa bam a hanyar jirgin wanda ya lalata layin dogo na jirgin lamarin da ya kai ga tarwatsa injin jirgin. Sannan ya ce sun bude wuta a daidai saitin direba da tankin mai.

'Yan bindiga sun saka Bam a layin dogon Abuja/Kaduna, Shehu Sani ya tsallake rijiya da baya
'Yan bindiga sun saka Bam a layin dogon Abuja/Kaduna, Shehu Sani ya tsallake rijiya da baya Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

Lamarin ya afku ne a tsakanin tashoshin Dutse da Rijana. Sai dai kuma ya ce direban ya yi nasarar jan jirgin zuwa tashar Rigasa.

A karshe sanatan ya yi kira ga dakatar da dukkan ayyukan jirgin kasa har zuwa lokacin da za a magance lamarin.

Read also

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

Ya rubuta a shafin nasa:

“A daren jiya, ‘yan bindiga sun kai hari kan jirgin kasa na Kaduna-Abuja. Sun dasa bam da ya lalata layin dogo na hanyar jirgin sannan ya tarwatsa gilashin iska na injin jirgin. Sun kuma bude wuta, inda suka fuskanci dirban da tankin mai. lamarin ya faru ne a tsakanin tashoshin Dutse da Rijana. Direban ya yi kokawan kai wa tashar Kaduna Rigawa.
“A safiyar yau. Ina cikin jirgin kasa lokacin da jirginmu ya yi karo da wani abun fashewar ya lalata hanyar jirgin. Saura kadan jirgin ya kauce daga layinsa, sai kawai muka tsallake rijiya da baya.
“Akwai bukatar dakatar da dukka ayyukan jiragen kasa na Kaduna Abuja a yau har zuwa lokacin da za a magance lamarin."

Jama'a sun yi martani:

Fahad Ibrahim Namorocco ya ce:

"Subuhanallah Allah yaqara kiyaye nagaba"

Mallam Sulaiman ya yi martani:

"Ya subhanallahi"

Bishop Net ya ce:

"Wannan abun bakin ciki ne... An gode Allah tunda ka tsira yallabai"

Read also

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

Adam Umar ya ce:

"Allah ya kyauta"

Rufai Sharif"

"Allah ya kiyaye gaba"

Shehu Sani ya bayyana wani sirri mai ban dariya game da matarsa da diyarsa

A wani labari na daban, mun kawo cewa tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya bayyana cewa a kodayaushe diyarsa kan dakile kokarin matarsa na ganin ta damki wayarsa.

Sanatan mara shayin magana wanda ya sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta People Democratic Party (PDP) a kwanan nan ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Ya rubuta: “A duk lokacin da na bai wa diyata wayata domin ta buga wasanni da shi, sai na lura cewa mahaifiyaryta ta kan so kiranta zuwa kicin; diyar tawa mai wayo sai ta mika mani wayar kafin ta tafi kicin din; toh daga nan sai ka ga mahaifiyar tana bata rai. Ina son diyata.”

Source: Legit

Online view pixel