Tunawa da EndSARS: Jami'an tsaro sun hana masu zanga-zanga kaiwa majalisar tarayya

Tunawa da EndSARS: Jami'an tsaro sun hana masu zanga-zanga kaiwa majalisar tarayya

  • Jama'a masu zanga-zangar EndSARS sun mamaye tituna da lungunan babban birnin tarayya na Abuja
  • Jami'an tsaro na DSS, Sojoji da 'yan sanda sun hana masu zanga-zangar isa majalisar tarayya a Abuja
  • Omoyele Sowore da Deji Adeyanju sun jagoranci masu zanga-zangar domin komawa Unity Fountain

FCT, Abuja - Wasu masu zanga-zangar EndSARS sun mamaye titunan babban birni tarayya a ranar Laraba domin tunawa da shekara 1 da yin asalin zanga-zangar.

Masu zanga-zangar sun tattaru a Unity Fountain, a Abuja kafin su fara bin kwararo, lunguna da kuma titunan Abuja, Daily Trust ta wallafa.

Tunawa da EndSARS: Jami'an tsaro sun hana masu zanga-zanga kaiwa majalisar tarayya
Tunawa da EndSARS: Jami'an tsaro sun hana masu zanga-zanga kaiwa majalisar tarayya. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

Omoyele Sowore, mawallafin jaridar Sahara Reporters ya na daga cikin wadanda suka yi jawabi ga masu zanga-zangar da ke rike da fastoci a Unity Fountain.

Read also

EndSARS: Babu wanda sojoji suka kashe lokacin zanga-zanga, Gwamnatin Tarayya

An ga 'yan sanda suna shawagi a kusa da masu zanga-zangar yayin da jama'ar suka bar wurin tare da tunkarar majalisar dattawa.

Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, Sojoji da kuma 'yan sanda sun hana masu zanga-zangar tunawa da EndSARS kai wa ga ginin majalisar tarayya.

Tun farko, masu zanga-zangar sun tattaru a Unity Fountain domin tunawa da shekarar da ta gabata da aukuwar zanga-zangar EndSARS, Daily Trust ta ruwaito.

Yayin da suke wurin, masu zanga-zangar sun bayyana rike da fastoci suna waka tare da kira ga gwamnati kan ta "biya musu bukatunsu".

Daga Unity Fountain, sun karasa tare da cigaba da tafiya domin tarar da majalisar tarayya.

Amma kuma, a kan hanyarsu ta zuwa majalisar tarayya, sun yi fito na fito da jami'an tsaro wadanda suka saka shinge.

Read also

Babu dan Najeriya mai tunanin da zai sake shiga zanga-zangar EndSARS, Hedkwatar Tsaro

Jami'an tsaron da ke dauke da bindigogi da bulalai, sun kara da rufe titunan da motocinsu. An ji masu zanga-zangar da aka ce su juya suna cewa "Zanga-zanga hakkinmu ce, mu ba bata-gari ba ne".

Bayan tattaunawar kusan sa'a daya tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar, babu wani cigaba da aka samu.

'Yan sanda sun tsaya tsayin daka kuma sun hana masu zanga-zangar karasawa majalisar tarayyan.

Daga bisani, dole ta sa jama'ar da ke zanga-zangar suka juya tare da sake tunkarar Unity Fountain, TheCable ta wallafa.

Omoyele Sowore, shugaban 'yan juyin juya hali da Deji Adeyaju, mai rajin kare hakkin dan Adam, su na daga cikin masu zanga-zangar.

Yadda 'yan sanda suka yi ram da masu zanga-zanga a Lekki Tollgate

A wani labari na daban, 'Yan sanda sun yi ram da a kalla mutum biyu da ke zanga-zanga a Lekki tollgate a Legas. Duk da jan kunnen da aka yi wa masu son yi tattakin cika shekara daya da yin asalin zanga-zangar, sun fito kwan su da kwarkwatarsu.

Read also

EndSARS: Yan sanda sun damke dan jaridar Legit a LekkiToll Gate

A safiyar Laraba, wasu mutane sun taru a tollgate inda jami'an tsaro a shekarar da ta gabata suka tarwatsa taron, Daily Trust ta wallafa.

Hakeem Odumosu, kwamishinan 'yan sandan jihar Legas tun farko ya ce jami'ansa su bar ababen hawa ne kadai a yankin Lekki ba wata zanga-zanga ba.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel