EndSARS: Yan sanda sun damke dan jaridar Legit a LekkiToll Gate

EndSARS: Yan sanda sun damke dan jaridar Legit a LekkiToll Gate

  • Jami'an tsaro a jihar Legas sun damke dan jaridar Legit.ng a Legas
  • Abisola Alawode ya dira Lekki Toll Gate don kawo rahoto kan zanga-zangar dake gudana a wajen
  • Kawai kafin ya ankara yan sanda sukayi masa ribiti, yanzu haka bai iya gani da ido daya

Jami'an yan sandan Najeriya a ranar Laraba, 20 ga Oktoba sun damke dan jaridar Legit.ng, Abisola Alawode, a filin tunawa da ranar zanga-zangar EndSARS a Oktoba 2020.

An damke Abisola ne a filin Lekki Toll Gate inda zanga-zangar ke gudana.

Abisola, wanda aiki ya kaisa wajen na kawo mana rahoto ne kan abubuwan dake gudana lokacin da yan sanda sukayi ram da shi.

Yan sanda sun bukaci yan jaridar su rataye katin shaidarsu kuma yana shirin haka kenan suka kwace kamarori da kayan aikinsa.

Read also

Da duminsa: Bam ya hallaka akalla mutum 32 a Masallacin Shi'a a ​kasar Afghanistan

Bidiyon lokacin da suka awon gaba da shi:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayi magana da sauran yan jarida dake aiki a wajen, Alawode ya bayyana cewa yanzu haka bayya gani da ido daya saboda sun bugesa.

Ya kara da cewa duk hujjojin da suka nuna shi dan jarida ne yan sanda suka kwace.

Daga karshe suka shiga dashi cikin bakar mota inda aka ajiye sauran wadanda aka damke.

Source: Legit

Online view pixel