EndSARS: Babu wanda sojoji suka kashe lokacin zanga-zanga, Gwamnatin Tarayya

EndSARS: Babu wanda sojoji suka kashe lokacin zanga-zanga, Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin tarayya tace sojoji ba su kashe ko mutum ɗaya ba daga cikin masu zanga-zanga a Tollgate, jihar Legas
  • Ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed, yace babu wata shaida ko da ta gawar mutum ɗaya ne, da aka kawo wa gwamnati
  • A cewar ministan an kashe sojiji shida da yan sanda sama da 30 a lokacin zanga-zangan amma sam bai dami kowa ba

Abuja - Gwamnatin tarayya tace bayan shekara ɗaya da zanga-zanga, har yanzun babu wata shaidar dake nuna cewa sojoji sun kashe mutane a Lekki Tollgate.

The Cable ta rahoto cewa a ranar 20 ga watan Oktoba, wasu sojoji sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga a Lekki Tollgate, jihar Legas, a kokarinsu da tarwatsa su.

Tun a wancan lokacin ake zargin cewa sojojin sun hallaka mutane tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Kara Kaɗa Hanjin PDP Kan Wanda Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

Lai Muhammed
Da Duminsa: Bayan shekara daya, babu shaidar sojoji sun kashe mutane a zanga-zangar EndSARS, Gwamnatin Buhari Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Laraba, Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya kira lamarin da, "kisan fatalwa."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ministan yace:

"Yau ne ranar farko na cikar lamarin kisan fatalwa shekara ɗaya a Lekki Tollgate dake jihar Legas, ko kuma ince zanga-zangar lumana daga baya yan ta'adda suka mamaye ta."
"Shekara ɗaya kenan, duk wannan lokacin da aka baiwa iyalan waɗanda suke zargin an kashe da kuma waɗanda suke zargin an yi kisan kiyashi, su kawo shaida, har yanzun shiru kake ji."
"Ba gawarwakin, babu iyalan kuma babu shaidu, wai ina kuke ne iyalan mutanen da aka kashe? Shin kun kai ƙara kotu ne? Idan kuma ba haka ba meyasa?"

Shin sojoji sun buɗe wuta a Tollgate?

Ministan ya kara da cewa sojoji ba su buɗe wuta kan masu zanga-zanga ba, lamarin a kafafen sada zumunta ne kawai aka yi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Gida Sun Kashe Basarake da Wasu 2 a Jihar Arewa

Vanguard ta rahoto ministan na cewa:

"Gwamnan tana alfahari da hukumomin tsaro bisa yadda suka ji da zanga-zangan da kuma rikicin da ya ɓarke, ta hanyar ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyi."
"Sojiji shida da yan sanda 37 da aka kashe lokacin EndSARS mutane ne kamar kowa suna da iyalai, duk da cewa ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun yi watsi da mutuwarsu."

A wani labarin kuma kun ji Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo a matsayin shugaban ƙasa ba

Ɗaya daga cikin jiga-jigan PDP, Raymond Dokpesi, yace ba dalilin da zaisa yan Najeriya su amincewa ɗan Igbo ya shugabance su.

Shugaban kamfanin DAAR yace kamata ya yi PDP ta sake baiwa Atiku Abubakar, daga yankin arewa maso gabas dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel