An sheke kwamandojin ISWAP 3, Yaya Ebraheem, Baba Chattimari, Abu Oubaida da wasu 21

An sheke kwamandojin ISWAP 3, Yaya Ebraheem, Baba Chattimari, Abu Oubaida da wasu 21

  • Sojin Najeriya sun halaka manyan kwamandojin ISWAP 3, Yaya Ebraheem, Baba Chattimari da Abu Adam Oubaida da wasu 21
  • Hatta mataimakin shugaban 'yan ta'addan na Sambisa, Modou Bacheer Oukocha ya sha da kyar da miyagun raunika
  • Wannan arangamar ta faru ne yayin da 'yan ta'addan suka kai wa tawagar sojin Najeriya hari a Ngamdu, Borno

Borno - A kalla mayakan ta'addancin 24 na ISWAP da suka hada da manyan kwamandoji aka kashe yayin da suka yi kokarin kai wa tawagar rundunar soja hari a Ngamdu, da yammacin Laraba.

PRNigeria ta tattaro cewa, daga cikin manyan kwamandojin da aka halaka akwai Yaya Ebraheem, Baba Chattimari da Abu Adam Oubaida.

Har ila yau, mataimakin Jaysh na ISWAP a Sambisa, Modou Bacheer Oukocha, ya na daga cikin wadanda suka samu miyagun raunika.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

An sheke kwamandojin ISWAP 3, Yaya Ebraheem, Baba Chattimari, Abu Oubaida da wasu 21
An sheke kwamandojin ISWAP 3, Yaya Ebraheem, Baba Chattimari, Abu Oubaida da wasu 21. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Wata majiyar tsaro daga cikin rundunar ta sanar da PRNigeria cewa, yayin da dakarun sojin kasa suka fara artabu da 'yan ta'addan, jiragen yakin rundunar sojin sama sun isa wurin inda suka fara sakin bama-bamai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce:

"Tawagar rundunar sojin na tafiya ne tsakanin Damaturu zuwa Maiduguri yayin da suka samu labarin harin sansaninsu na Ngamdu. Tuni tawagar ta juya sansanin bayan ta sanar da NAF.
"A kan hanyarsu ta zuwa Ngamdu, tawagar ta ci karo da 'yan ta'addan kuma sun fara musayar wuta. Ana tsaka da fadan ne sai jiragen yaki suka bayyana inda suka dinga kisan 'yan ta'addan."

A ranar Talata, miyagun 'yan ta'addan sun kai wa sansanin sojin Najeriya da ke Ngamdu farmaki. Da taimakon jiragen yaki da kuma sojin sama aka fatattake su.

Sojoji 4 sun sheka lahira, 1 ya jigata yayin arangama da 'yan ISWAP a Borno

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan ta'adda da shugabannin 'yan bindiga 12 da aka sheke a 2021

A wani labari na daban, a kalla sojoji hudu ne suka rasa ran su a ranar Talata yayin bankado harin da mayakan ISWAP suka kai garin Ngamdu, wani gari da ke tsakanin iyakar jihohin Yobe da Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa, majiya mai karfi daga rundunar ta ce harbin ya samu hafsan sojan ne yayin da ya ke kokarin bai wa bataliyarsa kariya daga 'yan ta'addan.

An ruwaito cewa hafsan sojan ya samu miyagun raunika. Amma kuma an kai shi asibitin sojoji inda ya ke samun sauki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel