Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

  • Tunde Bakare ya zauna daga shi sai Shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa
  • Fasto Bakare ya tabo batun zaben 2023, ya soki masu kawo siyasar bangaranci
  • ‘Dan siyasar yana ganin cancanta da farin jini ne ya kamata a duba ba yanki ba

Abuja - Limamin da ke jagorantar lamarin addinin kiristanci a cocin Citadel Global Community Church, Tunde Bakare, ya gana da Muhammadu Buhari.

Daily Trust ta kawo rahoton abin da Fasto Tunde Bakare ya fada bayan ya zauna daga shi sai shugaban Najeriyar a yau, ranar 15 ga watan Oktoba, 2021.

Tunde Bakare yana da ra’ayin cewa shugaban kasar da ake bukata a zabe mai zuwa shi ne duk wanda ya cancanta, wanda zai iya kai Najeriya ga nasara.

Read also

Zaben 2023: Ku daina yi mana barazana, Dattawan Arewa ga Kudancin Najeriya

Faston ya soki masu goyon-bayan tsarin karba-karba da nufin mulki ya koma yankin kudancin Najeriya. Sannan yace yana shawara kan batun yin takara.

Bakare ya yi wannan jawabi da yake zanta wa da 'yan jarida. Faston yace ya fada wa Buhari abin da ke masa kaikayi, bayan yace ba zai sake zuwa Aso Villa ba.

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari
Tunde Bakare Hoto: Pastor Bakare
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Arewa ba ta ci moriyar mulkin da ta ke tayi ba

Vanguard ta rahoto babban limamin yana cewa rashin wayewar siyasa ta jawo ake kukan mulki ya bar Arewa, a na shi ra’ayin hakan ba zai canza komai ba.

“Rashin wayewarmu ce ta fuskar siyasa da muke cewa mulki ya tafi Arewa ko Kudu. A maimakon a nemo wanda ya fi cancanta, ya dace, ya fi farin jini.”
“Ku saurare ni, da a ce yankin da shugaban kasa ya fito yana tasiri, da yanzu babu bangaren da ya kai Arewa arziki da cigaba a shekaru 61.” – Tunde Bakare.

Read also

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

Bakare yace an shafe shekaru 40 zuwa 41 ana samun ‘Dan Arewa a fadar shugaban kasa, amma a banza.

Bakare ya bada misali da Obasanjo da Jonathan

‘Dan siyasar ya kawo misalin da yadda Olusegun Obasanjo ya rike kudin jihar Legas a mulkinsa, da yadda Goodluck Jonathan ya gaza yi wa yankinsa komai.

Har ila yau, Bakare ya yi murna da kwaskwarimar da ‘yan majalisa suka yi wa dokar zabe ta yadda za a rika amfani da na’urorin zamani a tattara kuri’u.

Rikicin APC da PDP a Zamfara

Dazu ku ka ji jam'iyyar PDP tana kukan cewa ana shirin rusa mata hedikwata a Zamfara. Hakan na zuwa bayan an karbe ofishin PDP ta ke haya an ba APC.

Sakataren yada labarai na PDP na reshen Zamfara, Farouk Ahmad Shattima yace za a ruguza ofishin da suka kama haya bayan sun kashe Naira miliyan 10.

Read also

Tattalin arziki: Mataimakin Shugaban kasa, Osinbajo ya yi wa Gwamnan CBN kaca-kaca

Source: Legit

Online view pixel