Gas din girki ya fi karfin talakawa: 'Yan Benue sun rungumi aiki da icce da gawayi

Gas din girki ya fi karfin talakawa: 'Yan Benue sun rungumi aiki da icce da gawayi

  • Mazauna garin Makurdi, sun nuna tsananin damuwa kan hauhawan farashin iskar gas a yan kwanakin nan
  • A cewar rahotanni, mazauna garin sun yanke shawarar komawa ga amfani da icce da gawayi biyo bayan tsadar gas
  • Rahoton ya ci gaba da bayyana cewa a yanzu jama’a na kashe karin kudi wajen cika tukunyar gas dinsu a jihar, hakazalika sun yi korafi kan tsadar kananzir

Makurdi, Jihar Benue Mazauna garin Makurdi, sun yanke shawarar komawa ga aiki da icce da gawayi yayin da farashin iskar gas ke kara hauhawa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a gidan mai na Bolek a Makurdi, ana cika tukunyar gas na 12.5kg kan N8500 sabanin N4500 da ake siyarwa a farkon shekarar.

Kara karanta wannan

Kungiya za ta yi shari’a da Buhari, Ministoci 2 a kan yunkurin Gwamnati na sa ido a Whatsapp

Gas din girki ya fi karfin talakawa: 'Yan Benue sun rungumi aiki da icce da gawayi
Gas din girki ya fi karfin talakawa: 'Yan Benue sun rungumi aiki da icce da gawayi Hoto: Kehinde Adeola
Asali: Facebook

Wata mazauniyar garin, Jummai Kande, wacce ta kasance a gidan man don cika tukunyar 5kg, ta ce ta biya N4000 sabanin N1400 da take biya wajen siyar adadin a farkon shekarar.

Kande ta yi korafi:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Abun damuwa ne. Ban san ina wannan kasar ta dosa ba. Dole na koma ga gawayi a madadin gas saboda mutum bai san nawa za a siyar da gas ba a watan Disamba.
“Wannan ya kasance ne saboda farashin gas na kan hauhawa a yanzu. Makonni uku da suka gabata, na sayi wannan adadin akan N3000 kuma yanzu sai da na biya N4000.”

Hakazalika, wata kungiyar mata da suka zo daga nesa don tattara abubuwan da suka rage na wata bishiya da ta fado a kwatas din Lobi a Makurdi sun yi korafi.

Daya daga cikinsu, Victoria Elaibe, uwar yara takwas, ta ce bai zama abun mamaki ba cewa ita da sauran matan da ke neman ice sun zo ne daga wurare masu nisa na garin don diban iccen da za su yi girki.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Ta ce:

“Saboda farashin iskar gas da kananzir sun fi karfinmu ne. hatta, gawayi da muka dogara da shi ya yi tsada a yanzu ta yadda na N100 ba zai girka abinci sau guda ga iyalina ba.
“Ina zama a yankin kasuwa kuma sai da na zo tun daga chan don tattara wadannan iccen don girkina saboda ba zan iya siyan buhun gawayi kan N2500 ba.”

Haka kuma, Margret Cletus da Aunty Adams, su dukansu mazajensu sun mutu, sun barsu da yara takwas da biyar kowannensu sun hade da Elaibe.

Sun bayyana cewa sun rungumi ice don girki biyo bayan hauhawar farashin iskar gas da kuma rashin ba za su iya siyan kwalban kananzir kan N400 ba.

Adams ta kara da cewa:

“Samun iccen ma ba abu mai sauki bane. Kuna iya ganin yadda muke yawo don wannan. Dubi sama ku ga yadda wasu matan ke tseren zuwa nan don shiga cikin mu. Yanayin ba shi da dadi.”

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

A gefe guda, mun kawo a baya cewa masana sun gargadi 'yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba za su fara siyan iskar gas a kan farashi mai tsananin tsada.

Wannan kenan a cewar 'Yan kasuwa na Iskar Gas. 'Yan kasuwar sun nuna damuwar su kan karancin shigo da gas da ke haifar da hauhawar farashinsa.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, 'yan kasuwan sun yi gargadin cewa iskar gas mai nauyin kilo 12.5 da a halin yanzu ake sayar dashi sakanin N7,500 zuwa N8,000 na iya tashi zuwa N10,000 kafin watan Disamba idan ba a yi wani abu don magance tsadar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel