Rashin tsaro: Sojoji sun samu gagarumar nasara, sun hallaka ‘Yan bindiga rututu a kwana 13

Rashin tsaro: Sojoji sun samu gagarumar nasara, sun hallaka ‘Yan bindiga rututu a kwana 13

  • Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa ta kashe ‘Yan bindiga sama da 40 a Oktoba
  • Janar Benard Onyeuko yace sojojin kasar sun yi lugude a Sokoto da Kaduna
  • Sojojin sun hallaka ‘yan bindigan ne a cikin makonni biyun farkon watan nan

Abuja - Sama da ‘yan bindiga 40 aka kashe a jihohin Arewacin Najeriya. Sojojin kasar suka tabbatar da wannan a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, 2021.

Mukaddashin darektan tada labarai na sojojin kasa, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya shaida wa manema labarai wannan. Daily Trust ce ta kawo rahoton.

Da Birgediya Janar Benard Onyeuko yake magana a hedikwatar tsaro da ke birnin tarayya Abuja, yace sun samu galaba a kan ‘yan bindiga da ke addabar jama’a.

Janar Benard Onyeuko yake cewa sun kashe wasu ‘yan bindigan da ke jihohin Kaduna da Sokoto a yankin Arewa maso yammacin Najeriya a watan Oktoban nan.

Read also

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

Babban jami’in sojojin kasan yace dakarun sojojin sun samu wannan nasara ne daga ranar 1 ga watan Oktoba zuwa (ranar Laraba) 13 ga watan na Oktoba mai-ci.

Sojoji
Sojan kasan Najeriya Hoto: www.thisdaylive.com
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma rusa inda 'Yan bindiga suke buya

Benard Onyeuko yace baya ga hallaka ‘yan bindigan, sojoji sun ruguza wuraren da suke fake wa, yace hakan ya zama dole saboda irin barazanar da ake fuskanta.

Janar Onyeuko yace dakarun sojojin sama sun bada gudumuwa wajen lallasa wadannan ‘yan bindiga a cikin makonni biyu da aka yi ana ragagarzar miyagun.

“A daidai wannan lokaci kuma, an hallaka ‘yan bindiga da-dama, kuma an rusa inda suke buya a hare-haren jiragen sama da aka kai a wasu wuraren.”
“An tabbatar da nasarar luguden wutan da aka yi bayan an ga dacen da aka yi a wuraren.” - Janar Onyeuko

Read also

Daukar aikin sojin sama: Abubuwa 14 da wadanda aka zaba suke bukatar tanada nan kusa

Har ila yau, Janar Onyeuko ya yi bayani a kan sabon kokarin da sojojin kasa suke yi na kawo zaman lafiya a yankunan kudancin kasar da kuma Arewa ta tsakiya.

An rasa sojoji da 'yan sanda 170 a watanni uku

Wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewa sojoji sama da 100 da ‘Yan Sandan Najeriya kusan 70 aka aika lahira daga watan Yuli zuwan Satumban shekarar bana.

Mutane kimanin 1300 suka mutu a wannan lokaci, kuma yankin Shugaban kasa na Arewa maso yamma ne ya dauki mafi yawan kashe-kashen da aka yi a kasar.

Source: Legit.ng

Online view pixel