An kashe mutane fiye da 1, 300 yayin da Fadar Shugaban kasa ta ke cewa ana samun tsaro

An kashe mutane fiye da 1, 300 yayin da Fadar Shugaban kasa ta ke cewa ana samun tsaro

  • Wani bincike ya nuna cewa an kashe mutane 1, 150 a watanni uku a jihohin Najeriya
  • Wadanda aka hallaka daga Yuli zuwa Satumban bana sun hada da Jami’an tsaro 170
  • Kashe-kashen ya fi yawa a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso yammacin kasar

Nigeria - Mutane akalla 1, 153 aka hallaka, baya ga sojoji 105, ‘yan sanda 67 da jami’an kula da shiga da fice biyu da jami’in kwastam suka mutu a wata uku.

Wani bincike da kungiyar SBM Intelligence ta gudanar ya nuna cewa mutane kusan 1, 200 suka mutu tsakanin watan Yuli da Satumban 2021 a fadin Najeriya.

Jaridar Daily Trust tace ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram da ‘yan bindiga da sauran masu tada-tsaye ake zargi da laifin hallaka dubban mutane a jihohin kasar.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada umarni a daure ‘Dan wasan Bayern a kurkuku saboda tsohon rikici da Budurwarsa

Sauran wadanda suka mutu sun hada da ‘yan kungiyar asiri 27, masu fafutukar Biyafara 29. Har ila yau an kashe masu garkuwa da mutane 23 da ‘yan fashi 24.

A tsawon watannin nan uku, binciken ya nuna cewa jami’an tsaro na sa-kai akalla 10 sun mutu.

Taron tsaro Fadar Shugaban kasa
Shugaba Buhari da manyan Jami'an tsaro Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Arewa sun samu kaso mafi tsoka

A yankin Arewa maso yamma aka fi fama da wannan kashe-kashe, inda aka rasa mutane 961. Sama da 50% sun fito ne daga Zamfara, inda aka kashe mutum 495.

Yankin da ya zo na biyu a binciken kashe-kashen shi ne Arewa maso tsakiya. A nan ma an rasa mutane 646. Sannan an kashe mutane 336 a Arewa maso gabas.

Mutane 300 aka kashe a yankin Kudu

Kara karanta wannan

Yadda tsofaffin Gwamnoni, Sanatoci da wasu ‘Yan Najeriya suka dankare Biliyoyi a waje

Kashe-kashen da aka samu labari a bangaren Kudancin Najeriya ba su da yawa sosai. A Kudu maso gabas inda abin ya fi kamari, an hallaka mutane akalla 137.

Sannan kuma mutane 105 da 102 aka samu labari sun mutu a Kudu maso kudu da Kudu maso yamma.

A yankin Kudu maso gabas inda masu fafutukar Biyafara suke cigaba da hura wutar rikici, an kashe mutane 59 daga farkon Yuli zuwa watann jiya na Satumba.

Ana samun cigaba ta fuskar tsaro?

A ranar Talatar nan ne aka ji hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, yace gwamnatin tarayya ta na ganin cigaba a fannin tsaro a kasar nan.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, yace ba za a kamanta irin nasarorin da ake samu yanzu, da abin ya rika faru wa a gwamnatin da ta shude ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng