Budurwa 'Yar Najeriya Ta Koka Bayan Jami’an Tsaro Sun Kwace Mata Kilishi A Filin Jirgin Saman Amurka

Budurwa 'Yar Najeriya Ta Koka Bayan Jami’an Tsaro Sun Kwace Mata Kilishi A Filin Jirgin Saman Amurka

  • Wata budurwa ta koka kan yadda aka mata kwace bayan ta isa Amurka yayin da jami’an tsaro suka kwace mata kilishi
  • Budurwar mai suna Moyo Bakare ta bayyana yadda ita da mahaifinta suka bar Najeriya zuwa Ingila kafin wuce wa Amurka
  • Ta ce ta ji zafin yadda ta tanadi wannan kilishi na tsawon lokaci tun daga Najeriya zuwa Ingila har Amurka amma ba ta samu ta ci ba

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta yi guzurin kilishi zuwa kasar Amurka amma ba ta samu daman ci ba

Budurwar mai suna Moyo Bakare ta zo ziyara Najeriya, kafin komawarta sai ta sayi guzurin kilishi don yin amfani da shi a Amurka.

Budurwa 'yar Najeriya ta koka kan yadda jami'an tsaro suka kwace mata kilishi a filin jirgin saman Amurka
Budurwar Ta Ce Ta Ji Zafin Haka Bayan Jami’an Tsaro Sun Kwace Mata Kilishi Bayan Dakonshi Da Ta Yi. Hoto: TikTok/@moyo_b and Getty images/Pius Utomi Ekpei and Aaron Foster.
Asali: UGC

Amma bayan doguwar tafiya zuwa Amurka ba ta samu ta ci kilishin ba saboda jami’an tsaron Amurka sun kwace kilishin bayan isarta kasar.

Kara karanta wannan

Labari Ya Canja: Yan Sanda Sun Binciko Gaskiyar Yadda Wata Budurwa Ta Mutu a 'Hotel'

Budurwar ta bayyana yadda jami'an tsaron suka kwace mata kilishi

Moyo ta wallafa faifan bidyo inda ta bayyana yadda suka yi tafiyar da mahaifinta daga Najeriya zuwa Amurka, inda ta ce su suka fara isowa filin sauka da tashin jiragen sama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan sun bar Najeriya, sun wuce Ingila kafin su zarce zuwa Amurka, inda ta bayyana rashin jin dadinta kan kwace kilishin da jama’an tsaro suka yi a Amurka, Legit.ng ta tattaro.

Ta rubuta a faifan bidiyon kamar haka:

“Wannan tafiyar tan a da tsawo, har yanzu ina kan dawowa hayyaci na, Allah ya jikan kilishi na.”

Mutane da dama sun yi martini akan wannan faifan bidiyo da ta wallafa:

@eby:

“Duk tsawon rayuwa na, ban taba ganin wannan filin sauka da tashin jiragen ba kowa ba.”

@chinaza:

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Bar Iyayenta Don Rayuwa Da Saurayi a Daji, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

“Mutum na farko a filin sauka da jirage, ya yi kyau!.”

@Niffybanco:

“Ya fi kyau ki je can da wuri akan ki je a latti, cunkoson Lagos ba a kauce masa.”

@Simon Simons:

“Shin sun baki kilishin ki?”

Budurwa Ta Kadu Bayan Ta Biya Kudin Haya N500k Ashe Ya Siyar Da Gidan Ya Bar Kasar

A wani labarin, wata budurwa 'yar Najeriya ta sha mamaki bayan ta biya kudin haya N500,000.

Ta ce biyan kudin ke da wuya ta na kokarin dawowa gidan sai ta samu labarin cewa ai an dade da siyar da gidan.

An kuma bayyana mata cewar mai gidan bayan siyar da gida ya dade da barin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel