Yar Najeriya Za Ta Auri Baturen Da Suka Hadu a Intanet Bayan Shafe Shekara 10 Ba Tare Da Miji Ba

Yar Najeriya Za Ta Auri Baturen Da Suka Hadu a Intanet Bayan Shafe Shekara 10 Ba Tare Da Miji Ba

  • Wata ‘yar Najeriya ta ba da labarin soyayyar da ke tsakaninta da masoyinta farar fata, wanda ta hadu da shi ta yanar gizo
  • Tosin, kamar yadda aka santa a TikTok, ta ce ta shafe kusan shekaru 10 babu aure kafin ta haɗu da mutumin mai suna Kieron a shekarar 2020
  • Sun yi soyayya sosai ta yanar gizo, kafin daga bisani suka haɗu ido da ido inda yanzu haka kuma ake maganar aure

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata ‘yar Najeriya ta ba da labarin yadda ta haɗu da wani bature da take shirin aura yanzu haka.

A cikin bidiyon da ta ɗora a TikTok, matar mai suna Tosin, ta bayyana cewa ta shafe kusa shekaru 10 ba tare da aure ba kafin haɗuwarta da baturen.

'Yar Najeriya ta hadu da farar fata da za ta aura a shafin kulla soyayya
'Yar Najeriya da ta shafe shekaru 10 ba miji ta za ta auri wani bature. Hoto: @kosinfinityandbeyond
Asali: TikTok

Ta haɗu da saurayin nata a shafin kulla soyayya

Kara karanta wannan

"Na Yi Babban Rashi": Budurwa Ta Koka Bayan Saurayin Da Ta Tsaya Yi Masa Jan Aji Ya Auri Wata Daban

Tosin ta ce ta haɗu da masoyin nata mai suna Kieron a dandalin ƙulla soyayya mai suna Bumble, a shekarar 2020, lokacin Covid-19, inda daga nan suka fara soyayya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ƙara da cewa bayan nan ne suka haɗu ido da ido inda suka ƙulla soyayyar sosai wacce tayi ƙarfin da suke jin ba ma za su iya rayuwa ba tare da juna ba.

Ta kuma ce ya ɗauke duka nauyinta yana biya mata buƙatunta na yau da kullum.

A yanzu haka Kieron ya nemi amincewarta kan ta aure shi wanda tuni ta amince da ɓuƙatar tasa.

Ga bidiyon kamar yadda ta ɗora shi a shafinta na TikTok:

Martanin masu amfani da TikTok bayan da 'yar Najeriya ta bayyana cewa zata auri farar fata

Da yawa daga cikin mabiyanta sun tofa albarkacin bakunansu dangane da wannan lamari na farin ciki da ya sameta.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Auri Attajirin Da Yake Ba Ta N50k Duk Wata, Ta Yi Korafin Cewa Ya Cika Mako

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin maganganun da mabiyanta suka yi.

@Millyalmodovar ta ce:

“Nima a Bumble na haɗu da saurayina”

@Misandrist Musings ya ce:

“Domin Allah ina son ganin baƙar mace ta samu soyayya ta gaskiya, hakan ya yi miki kyau.”

@spooky_for_the_wynne ya ce:

“Ku duka biyun kun burgeni, akwai ƙauna mai yawa a tsakaninki da shi.”

Dan Kanon da ya auri baturiya ya shiga aikin soja

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton matashin nan ɗan Kano Suleiman Isah da ya auri baturiya, kan shiga aikin soja da ya yi a Amurka.

Suleiman ya wallafa hoto sanye da kakin sojan Amurka a shafinsa na Fesbuk, wanda ke nuni da cewa ya shiga aikin soja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng