Babu Batun Daukar Ma’aikata: Yadda Wani Mutum Ya Ci Abinci a Otal Din da Mutum-Mutumi Ke Cinikayya

Babu Batun Daukar Ma’aikata: Yadda Wani Mutum Ya Ci Abinci a Otal Din da Mutum-Mutumi Ke Cinikayya

  • Wani bidiyon da aka yada a TikTok ya nuna wani gidan cin abinci da babu alamar mutum, sai dai mutum-mutumi
  • Bidiyon ya nuna yadda wani mutum ya zo ya ba da odar abinci, mutum-mutumi ya dauko ya kawo masa kamar mutum
  • Ba sabon abu bane ganin irin wadannan abubuwa a kasashen waje, musamman yadda fasahar zamani ke kara yaduwa

A wani bidiyon da aka yada, an gano wani gidan cin abinci da kwastomomi ke odar abinci ta hanyar sanar da mutum-mutumi ba dan Adam ba.

Bidiyon da @notkevinlasean ya yada a TikTok ya nuna yadda gidan cin abincin mai suna Robot Restaurant da ke birnin Tokyo a Japan ke harkallarsa.

Martanin jama'a game da gidan cin abinci mai 'robot'
Gidan cin abincin da na'ura ke aiki | Hoto: @kevinlasean
Asali: TikTok

Mutum-mutumi mai kawo abinci

Bidiyon ya fara ne yayin da wani mutum ya kira mai kawo abinci; wanda yake mutum-mutumi tare da ba da odar nau’in abincin da yake bukata.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Yan Bindiga Sun Sheke Mutane 10 a Zamfara, Gwamna Ya Yi Allah Wadai Da Harin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan bidiyon ya yanke zuwa wani wurin, inda aka nuna mutum-mutumin dauke da faranti cike da abinci ya nufi teburin da mutumin ke zaune.

Babu sauran ciwon kai

Shi kansa kwastoman, ya yi mamakin yadda mutum-mutumin ke aiki cikin tsanaki ba tare da samun wani tsaiko ba.

Bidiyon dai ya dauki hankalin mutane da yawa a kafar sada zumunta, inda suke bayyana ra’ayoyinsu ga wannan fasahar.

Wannan dai ba sabon abu bane a birnin Tokyo, domin akan yi yawan karo da shagunan siyar da abinci da sauran wurare da dama da ke amfani da mutum-mutumi.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

@Potatocat:

“Kalli yadda su uku suke kallonka.”

@zee74848:

“Ya za a yi idan masifaffiya irin Karen ta shigo ta fara tsawa ga mutum-mutumi.”

@user4758588484:

“Dan uwa sai waka yake a cikin zuciyarsa.”

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Abba Gida Gida Ya Cigaba da Rusau, Ya Ruguza Ginin Otel a Kano

@Jullen:

“Yanzu kenan babu wanda zai samu sana’a.”

@egm657:

“Kamar wurin su Sam da Cat.”

@JODIO:

“Za ka iya duba kudaden haraji na, sh ne abin da ya bani dariya.”

@Marle:

“Ba zai yiwu ba, dan uwa ka bi a hankali.”

A wani lokaci baya, mun kawo maku rahoton yadda wani gidan cin abinci ke amfani da mutum-mutumi wajen kula da gidan abinci a wata kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel