Najeriya da Wasu Ƙasashe 5 da Ke Amfani da Harshen Hausa da Baku Sani Ba

Najeriya da Wasu Ƙasashe 5 da Ke Amfani da Harshen Hausa da Baku Sani Ba

Yaren Hausa na daya daga cikin manyan yarukan Najeriya da suka hada da Yarbanci da Igbo a Kudancin kasar.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ba iya Najeriya ko kuma Arewacin kasar kadai ake yaren Hausa ba, ya kasance daya daga yarukan da ke kara fadada a kasashen ketare.

Kasashen da ke da masu yaren Hausa bayan Najeriya
Bayan Najeriya, Hausawa sun bazu zuwa sauran ƙasashen duniya musamman na Afrika. Hoto: The African History.
Asali: Facebook

Yadda Hausawa suka bazu a Nahiyar Afrika

Akwai Hausawa da dama a ƙasashen Afirka da kuma wadanda suka je neman ilimi ko kasuwanci a sauran ƙasashen duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tribune ta tabbatar da cewa akwai wadanda suke yaren Hausa aƙalla miliyan 70 a fadin duniya gaba daya.

Kara karanta wannan

Shirin ba ɗalibai rancen kuɗi; Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban NELFund

Legit Hausa ta jero muku kasashen Nahiyar Afirka da ke da yawan Hausawa waɗanda ke rayuwa a kasashen.

1. Najeriya

Mafi yawan Hausawa da ke Najeriya mazauna Arewacin Najeriya ne wadanda ke rayuwa a yankin tun tali-tali, cewar Britannica.

An fara koyar da harshen Hausa a Arewacin kasar a shekarar 1885 bayan bincike da ɗan ƙasar Jamus, J.F Schon ya yi.

Ingantacciyar Hausa a Najeriya ita ce Hausar Kano wacce ta kasance cibiyar kasuwanci da ke Arewacin kasar.

Sauran jihohin Hausawa a Arewacin kasar sun hada da Katsina da Sokoto da Zamfara da Kebbi da Jigawa da Kaduna.

2. Nijar

Bayan wasu yaruka da ke kasar, akwai masu yaren Hausa fiye da miliyan 10 a kasar, cewar legacy Export.

Mafi yawan 'yan ƙasar suna magana da Hausa a bangaren kasuwanci da harkokinsu duk da a hukumance Faransanci shi ne yaren kasar.

Al'adun kasar kusan iri daya ne da na takwarorinsu Hausawa da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hare haren 'yan bindiga: Basarake a Zamfara ya 'tona' asirin masu ruruta ta'addanci

3. Ghana

Hausawa sun kafu a kasar tun shekaru 50 da suka wuce ta hanyar kasuwanci da cinikin bayi, GhanaWeb ta tattaro.

Mafi yawan Hausawa da ke Ghana Musulmai ne da yawanci ke bin darikar Tijjaniya da Ƙadiriyya.

4. Chadi

Chadi da ke Arewacin Afirka na da Hausawa fiye da 100,000 daga cikin mutane miliyan shida da ke kasar.

Ana daraja Hausawa a Chadi saboda rikon addini da suke dashi da kuma kwarewa a kasuwanci.

Hausawa sun samu wurin zama ne a kasar a ƙarni da 19 zuwa 20 yayin zuwa kasar Saudiyya domin yin aikin hajji.

5. Sudan

Mafi yawan Hausawa da ke Sudan Musulmai ne da ke sanya jallabiya a matsayin kayan sakawa kamar yadda al'adar kasar ta ke.

Akwai wani kogi a kasar da ake kira 'Kano-Borno-Darfur-Red Sea' da Hausawa da Fulani da kuma Kanuri suka bi hanyar domin zuwa kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Katsina: An shiga makoki bayan 'yan bindiga sun hallaka shugaban APC da wani mutum

6. Benin

Tun kafin hada Arewaci da Kudancin Najeriya a 1914, Hausawa suke Benin domin harkokin kasuwanci, cewar allAfrica.

Tarihi ya nuna cewa Hausawa 'yan farauta ne suka fara zuwa kasar saboda arzikinta kafin daga bisani wasu su biyo baya.

Sarkin Hausawan Benin na farko, Malam Adamu mafarauci ne daga Ningi a jihar Bauchi wanda aka zaba saboda jarumtarsa da kwarewa a farauta.

Yawan masu magana da Hausa a Najeriya

Kun ji cewa rahotanni sun tabbatar cewa yawan masu magana da harshen Hausa a Najeriya ya kai kimanin miliyan 120.

An bayyana haka a taron da sashen harsunan Afrika da al’adu, na jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria jihar Kaduna suka shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel