Elon Musk Zai Mayar Da ’Yan Twitter Su Zama Attajirai, Ya Ware N2bn Zai Fara Raba Musu, Ya Fadi Sharadi

Elon Musk Zai Mayar Da ’Yan Twitter Su Zama Attajirai, Ya Ware N2bn Zai Fara Raba Musu, Ya Fadi Sharadi

  • Elon Musk, mai kamfanin Twitter, ya yi alkawarin fara biyan masu kirkire cikin makwanni masu zuwa yayin da yake ci gaba da yin sauye-sauye a kamfanin
  • Musk ya kuma bayyana cewa zubin farko na biyan zai kai kusan dala miliyan 5, kuma komai a shirye yake
  • Sai dai, ba kowa ba ne zai amfana daga tsarin, saboda ya kafa sharudda ga masu sha'awar samun kudi a Twitter

Twitter, fitacciyar kafar sada zumunta, na shirin gabatar da wani sabon shirin da zai bai wa jama'ar da ke da dangwalen 'verification' damar samun kudi a kafar.

Elon Musk, mamallakin kamfanin da ya saye shi a watan Oktoban bara ne ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A cewarsa, ana sa ran zubin farko na kudin da zai biya zai kai kusan dala miliyan 5 wanda ya kai kimanin Naira biliyan 2.3.

Kara karanta wannan

Ni ba barawo bane: Sanatan APC ya sharbi kuka a majalisa, ya fadi sharrin da aka masa

Yadda Elon Musk zai fara biyan kudi ga 'yan Twitter
Elon Musk, mai kamfanin Tesla da Twitter | Hoto: adda247.com
Asali: UGC

Sai dai, Musk ya jaddada cewa masu tabbataccen asusu ne kadai za su ci gajiyar wannan shiri, kamar yadda rahotannin CNN suka bayyana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Me yasa Elon Musk zai fara biyan masu amfani da Twitter kudi?

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Twitter ke fuskantar kalubale wajen rike masu ba shi talla bayan da ya yi koran ma’aikata da yawa.

Sayen da Elon Musk ya yiwa Twitter ya jawo raguwar amintar masu daura talla, yayin da suke shakkar sanya tallansu akan dandamalin.

Bugu da kari, kaddamar da cajin $8 kowane wata ga masu asusun da ke da dangwalen ‘verified’ ya gamu da turjiya da suka daga fitattun ‘yan soshiyal midiya.

Ta yaya biyan kudin zai yi aiki?

Musk ya yi cikakkun bayanai game da shirin biyan kudin yana mai bayyana cewa za a fara biyan masu asusun da ke da ‘verification’ nan da 'yan makwanni kuma ya bayyana cewa za a biya su kudi ne kan tallan da aka nuna a kan shafukansu.

Kara karanta wannan

Godwin Emefiele: Shin Shugaban Kasa Bola Tinubu Na Da Ikon Dakatar Da Gwamnan CBN? Lauya Ya Yi Bayani

Wannan ne dai karon farko da Twitter zai fara irin wannan lamari, yayin da kamfanonin sada zumunta irinsu Facebook suka jima da fara biyan masu talla.

An yi ta cece-kuce a kafar Twitter lokacin da Musk ya bayyana fara karbar kudi kan duk wani asusun da ke neman ‘verification’.

Cikin sa’o’i kadan da dakatar da Facebook, Zuckerberg ya tafka asarar $6bn

A wani labarin, wanda ya kirkiro kafar sada zumuntar Facebook, Mark Zuckerberg ya tafka asarar fiye da $6,000,000,000 cikin sa’o’i kadan da dakatar da kafar.

Lamarin da ya janyo asarar ta auku ne cikin sa’o’i kadan kwatsam kafafen sada zumuntar zamani kamar Facebook, Messenger, Instagram da WhatsApp su ka tsaya cak su ka dena yin aiki.

Kamar yadda Yahoo Finance ta ruwaito, wannan lamarin da ya auku a ranar ranar Litinin 3 ga watan Oktoban 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel