‘Dan Baiwa Ya Yi Cin Kaca a Jarrabbawar JAMB, Ya Tashi da 99 Cikin 100 a Lissafi

‘Dan Baiwa Ya Yi Cin Kaca a Jarrabbawar JAMB, Ya Tashi da 99 Cikin 100 a Lissafi

  • Wani matashi mai shekara ya ci maki 337 a jarrabawar UTME da hukumar JAMB ta saba shiryawa
  • Master Lotanna Azuokeke ya rasa maki 1 ne rak a jarrabawar lissafi, Ingilishi ya bata masa lissafi
  • Dalibin yana da burin digiri a jami’ar UNN ta Nsukka, abin da yake so shi ne zama Injiniyan wuta

Wani dalibi da yake karatu a makarantar Bishop Otubelu Juniorate da ke Trans Ekulu a jihar Enugu, ya bada mamaki a jarrabawar UTME.

The Nation ta ce Master Lotanna Azuokeke ya ba mutane tsoro da ya ci maki har 99 a cikin 100 a darasin lissafi a jarrabawar nan ta bana.

Master Lotanna Azuokeke mai shekara 15 ya tashi da maki 337, abin da ya zarce 84.2% na maki 400 da ake iya samu a wannan jarrabawa.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Babban Lauya Ya Ba Wa APC Da Yan Najeriya Muhimmin Shawara Kan Kujerar Kakakin Majalisa

A darasin Chemistry, matashin yana da maki 88, sannan ya samu 86 a Physics. Hakan ya nuna irin kwakwalwar da Ubangiji ya yi masa.

Ingilishi ya nemi yin gardama

Inda abin ya zo da tangarda shi ne a sashen Ingilishi, Master Azuokeke ya samu 64. Ingilishi dole ne ga kowane mai rubuta jarrabawar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr Chiwuike Uba ya fitar da jawabi a madadin wanda ya kafa makarantar, Bishop Otubelu Juniorate, ya bada labarin wannan dalibin.

Azuokeke
Master Lotanna Azuokeke Hoto: Jamb official, Igbere TV
Asali: Facebook

Yaron Oba ya zama abin alfahari

Mai magana da yawun bankin babban limamin darikar Angilikan na Kiristoci a Nike, ya nuna su na matukar alfahari da Master Azuokeke,

Sanarar Dr. Uba ta nuna dalibin asalinsa mutumin kauyen Oba ne a garin Idemmili a Anambra.

A jarrabawar wannan shekara aka karya tarihin da Chidera Obi ta bari shekaru biyar da suka wuce, bayan ita kuma ta samu maki 329 a UTME.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Fitar da Shafuka 90 a Kan Jerin Nasarorin da Buhari Ya Samu

Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce Azuokeke ya na neman gurbin karantar ilmin Injiniyancin wutar lantarki a jami’ar Najeriya da ke Nsukka.

A Oktoban 2008 aka kafa wannan makaranta da yara 24 kacal, yanzu ta na da dalibai 411, daga cikinsu har da wadanda suka yi zarra a Najeriya.

'Yan Najeriya a Sudan

Rahotanni sun ce jirage biyu suka sauka a daren Alhamis a filin sauka da tashi na Nnamdi Azikwe a Abuja dauke da 'Yan Najeriya daga Sudan.

Jirgin saman sojin ruwa ya ɗauko mutum 94, jirgin kamfanin AirPeace ya ɗauko mutum 283, yanzu ‘Yan Najeriya sama da 1, 000 suka rage.

Asali: Legit.ng

Online view pixel