Bidiyon Wata Mata Na Tallar Ruwa Dauke Da Tagwayenta Ya Sosa Zukata

Bidiyon Wata Mata Na Tallar Ruwa Dauke Da Tagwayenta Ya Sosa Zukata

  • Bidiyon wata mata ƴar Najeriya goye da tagwayenta yayin da take siyar da ruwan leda a bakin titi ya sosa zukatan mutane
  • A cikin wani bidiyo mai ban tausayi, matar na ɗauke da tagwayen tana tafiya kan titin da sauri
  • Da suke tsokaci akan bidiyon, masu amfani da yanar gizo sun tausaya mata inda suka nuna niyyar su ta taimaka mata da kuɗi

Masu amfani da soshiyal midiya sun yi tsokaci sosai kan wani bidiyon wata mata ƴar Najeriya tana neman na abinci.

A bidiyon wanda ya yaɗu, an nuna matar tana talla a bakin titi ɗauke da tagwayen ta.

Tagwaye
Bidiyon Wata Mata Na Tallar Ruwa Dauke Da Tagwayenta Ya Sosa Zukata Hoto: TikTok/@favecreativeconcept
Asali: TikTok

Matar mai tsantsar nuna kula ga ƴaƴanta ta goya ɗaya daga cikin su a bayan ta yayin da ta ɗauki ɗayan a gaba.

Lokacin da aka tambayeta ta bayar da labarinta, matar ta bayyana cewa mahaifin su ya gudu ya bar su jim kaɗan bayan an haife su.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Tsoho Yayi Awon Gaba da Wayoyin Mutane 70

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutane sun yi tsokaci

Masu amfani da soshiyal midiya sun yi sharhi sosai kan bidiyon inda wasu da dama daga ciki suke da niyyar su taimakawa matar.

Ga kaɗan daga ciki:

@chinenyeiroha ta rubuta:

"Ina cikin takaici yanzu, dubi abinda ni da mijina muke nema, sannan har mahaifin su zai iya guduwa yar bar su, dan Allah ina son na taimaka musu."

@ivieroyal25 ya rubuta:

"Wasu mutanen kuma sai suyi ta zagin mata masu kula da yara su kaɗai, kalli irin halin da suke shiga."

@lucyernest3 ta rubuta:

"Dan Allah ki tuntuɓe ni ƴar'uwa ina son na taimakawa matar nan. Shin akwai hanyar da zan iya tuntuɓar ki?"

@hawanatukanu1 ta rubuta:

"Lokacin da ƴaƴan zasu zama wani abu sannan mahaifin kamar daga sama zai zo neman yafiya."

@hairbymacanny ta rubuta:

Kara karanta wannan

Maza Tsada Suke", Kyakkyawar Budurwa Ta Fita Neman Saurayi Tace Ta Gaji Da Zama Ba Mashinshini

"Ni mahaifiya ce mai tagwaye mata sannan na san irin wahalar da ake sha wajen kula da yara, balle kuma a irin halin da take ciki. Allah ya kawo mata ɗauki."

Bayan Shekara 8 Suna Zaman Dadiro, Wasu Masoya Sun Rabu Da Juna

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta koka kan yadda saurayin ta ya rabu da ita bayan sun kwashe suna cin moriyar juna tare.

Budurwar ta koka kan hakan inda ta bayyana wani abu da saurayin nata yayi mata da bata ji daɗin sa ba a yayin raubuwar su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel