"Maza Tsada Suke", Kyakkyawar Budurwa Ta Fita Neman Saurayi Tace Ta Gaji Da Zama Ba Mashinshini

"Maza Tsada Suke", Kyakkyawar Budurwa Ta Fita Neman Saurayi Tace Ta Gaji Da Zama Ba Mashinshini

  • Wata budurwa mai neman saurayi ta janyo cece-kuce kan yadda ta nuna ruwa a jallo tana neman mashinshini
  • Budurwar ɗauke da wani allo ta rubuta abinda take buƙata, yayin da take ta zagayawa cikin ɗan wani waje da ƙarfin guiwarta
  • Mutane da dama sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan hanyar da budurwar ta bi wajen neman saurayi

Wata kyakkyawar budurwa ta fita neman saurayi ɗauke da wani allo inda ta nuna aniyar ta na fara soyayya.

A wani bidiyo da ya karaɗe manhajar TikTok, budurwar wacce ke sanye da jajayen kaya tana riƙe da wani allo a saman kanta wanda aka rubuta 'Bani da saurayi a shirye nake na samu masoyi'.

Budurwa
"Maza Tsada Suke", Kyakkyawar Budurwa Ta Fita Neman Saurayi Tace Ta Gaji Da Zama Ba Mashinshini Hoto: TikTok/@Bushra_saksi
Asali: TikTok

Budurwar tana ta murmushi abin ta kamar wata mai tallar kaya ga kwastomomi. Tana ta ɗan kewaya wa ba tare da damuwa da irin kallon da mutane suke yi mata ba.

Kara karanta wannan

"Ina Da Ikon Naɗa Duk Wanda Na So Har 29 Ga Mayu" Gwamnan PDP Ya Maida Martani

Bidiyon nata ya ɗauki hankula sosai a soshiyal midiya. Wasu sun yi tunanin cewa kawai ta fito neman suna ne yayin da wasu kuwa sun kaɗu sosai kan yadda akai har ta iya yin hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga kaɗan daga ciki:

@Reasonable ya rubuta:

"Kowane jinsi tsoron ɗayan jinsin yake yi yanzu, kowa so yake ya tsaya shi kaɗai, baya son rigima."

@noagbehenkel12 ya rubuta:

"Daga wannan shekarar zuwa gaba, ƴanmata zasu fito neman samari fiye da haka."

Geraldoh ya rubuta:

''Halayen irin namijin da kike buƙata. Shin ko zamu iya fita shan lemu domin mu san juna sosai."

@ifeanyiechefu ya rubuta:

"Wai har ƙarancin mazajen aure ya kai haka?"

@Apeh Martin ya rubuta:

"Wai har abin ya kai hakan kenan, kiyi haƙuri ƴar'uwa komai zai daidaita nan bada jimawa ba."

Taron Biki Ya Tarwatse a Benin Bayan Amarya Ta Gano Ango Yana Da 'Ya'Ya 7

Kara karanta wannan

Ba dani ba: Bidiyon budurwa ya girgiza matasa, ta ce ba za ta auri mai albashin N70k ba

A wani labarin na daban, wani taron biki ya tashi ba a shirya ba bayan amarya ta gano wani ɓoyayyen sirrin ango a ranar biki.

Amaryar ta gano cewa ashe angon nata maƙaryaci ne kuma ya ɓoye mata wani sirri wanda yakamata ace ta sani a matsayin ta na wacce zai aura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel