Amarya Ƴar Ƙasar Ghana Ta Samu Kyautar iPhone 14 Pro Max, Da Miliyoyin Kuɗi

Amarya Ƴar Ƙasar Ghana Ta Samu Kyautar iPhone 14 Pro Max, Da Miliyoyin Kuɗi

  • Wata amarya ƴar ƙasar Ghana ta samu wata gagarumar kyauta a ranar ɗaurin aurenta wacce ta ɗauki hankulan mutane a yanar gizo sosai
  • Tsaleliyar amaryar ta samu kyautar waya ƙirar iPhone 14 pro max, miliyoyin kuɗi da tsadaddun kyautuka na alfarma
  • Bidiyon kyautar da aka yiwa amaryar ya yaɗu sosai inda mutane da dama suka tofa albarkacin bakin su kan irin wannan kyauta da aka yi mata

Wata kyakkyawar amarya ƴar ƙasar Ghana tayi gamo da katar ranar auren ta inda aka gwangwajeta da kyautar maƙudan kuɗaɗe.

Tsaleliyar amaryar ta samu kyautar €10,000 (N4.8m) da sauran kyaututtuka na gani na faɗa a wajen bikinta a wani bidiyo wanda ya ɗauki hankulan mutane sosai a yanar gizo.

Amarya
Amarya Ƴar Ƙasar Ghana Ta Samu Kyautar iPhone 14 Pro Max, Da Miliyoyin Kuɗi Hoto: Instagram/live_weddings_with_kwaku
Asali: Instagram

A cikin ɗan gajeran bidiyon wanda Legit.ng ta ci karo da shi, amaryar ta karɓi kyautar tsaɓar kuɗin, iPhone 14 pro max, da takalmi mai tsini ƙirar Jimmy Choo, daga hannun wani mutum wanda yayi wata shiga ta gani ta faɗa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gidan, Sun Harbe Shugaban Jam'iyya Har Lahira

Shafin @live_weddings_with_kwaku wanda ya sanya bidiyon bikin a Instagram, yace mijinta ne ya gwangwaje ta da kyautar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun rubuta cewa:

Ango ya bayar da kyautar €10,000, iPhone 14 pro max, takalmi mai tsini ƙirar Jimmy Choo a matsayin kyautar biki."

Bidiyon ya ɗauki hankula

Sama da mutum dubu uku suka kalli bidiyon wanda ya samu sharhin sama da mutum ɗari a zuwa daidai lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ga kaɗan daga ciki:

Nenye_eve_ramona ta rubuta:

"Wow tirƙashi"

Shirleysnailand_beautylounge ta rubuta:

"Ina taya ki murna ƴar'uwa."

"Yunwa Ta Kusa Kashe Ni" Ƴar Najeriya Mai Karatu a Ƙasar Waje Tayi Guzurin Kayan Abinci, Bidiyon Ya Yaɗu

A wani labarin na daban kuma, wata ƴar Najeriya mai karatu a ƙasar waje tace ta koyi darasi bayan da ta ɗanɗani kuɗar ta a hsnnun yunwa a ƙasar da take karatu.

Budurwar tace ba zata ƙara yin saki na dafa ba inda ta kinkimi kayan abinci ta shilla da su can ƙasar domin gudun kada tarihi ya sake maimaita kan sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel