Budurwa ta baka wa tsohon saurayinta da sabuwar masoyiyarsa wuta suna tsaka da bacci

Budurwa ta baka wa tsohon saurayinta da sabuwar masoyiyarsa wuta suna tsaka da bacci

  • Wata mai suna Sarah yar kasar Australia ta banka wa tsohon saurayinta da sabuwar budurwarsa wuta suna tsaka da bacci
  • Bayanai sun nuna cewa ta shiga gidan ta watsa Fetur, ta cinna wuta, ita da saurayin ɗan Najeriya sun mutu
  • Bincike ya nuna cewa Sarah ta murza soyayya mai matukar rudani da mutumin, kuma har ƴaƴa suka haifa lokacin da suke tare

Australia - Wata budurwa yar ƙasar Autralia, Sarah Mudge, ta banka wa tsohon saurayinta ɗan Najeriya, Stanley Obi, da budurwarsa, wuta suna tsakiyar bacci.

Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, kamar yadda bayanan yan sandan ƙasar ya nuna.

Bayanai sun nuna cewa Mista Stanley na cikin gida tare da masoyiyarsa yayin da Sarah ta je cikin gidan dake Bidyan Boulevard a Logan, kudancin Brisbane, ta watsa man fetur kuma ta cinna wuta.

Kara karanta wannan

Zan hadu da rabo na: Mai digirin da ke tallan 'yan kamfai ya ce bai fidda rai da yin arziki ba

Matsalar soyayya
Budurwa ta baka wa tsohon saurayinta da sabuwar masoyiyarsa wuta suna tsaka da bacci Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Saurayin ya rasa rayuwarsa da daren ranar bayan ya samu ƙuna a sama da kaso 90 cikin 100 na jikinsa, yayin da budurwar ta tsira da karamar kuna a maƙogwaronta.

Rahoto ya nuna cewa ita kanta, Sarah ba ta tsira daga wutar a raye ba, kuma tsofaffin masoyan suna ƴaƴa lokacin da suke tare.

Yadda lamarin ya faru

Maƙotan saurayain sun bayyana yadda suka ga mummunan lamarin da ya faru da idanuwan su, da kuma ganin su da shi na ƙarshe.

Ɗaya daga cikin makotansa ya ce:

"Na farka na ji wani na roko ta gilashin kofa, bana ji sosai, amma naji yana faɗin ku kira yan sanda. Na kunna haske ta yadda na ga wani mutumi tsirara, yana roƙo ta gilashin kofa, ku kira yan sanda, ku kira yan sanda."

Kara karanta wannan

Ta Kacame: Mai Garkuwa Ya Yi Ƙorafi a Kotu, Ya Ce Abokansa Sun Cuce Shi Sun Bashi N200,000 Kacal Cikin N12m Da Suka Samu

"Saboda kunna hasken da na yi na gane ashe Stan ne maƙoci na, lokacin da na kalle shi ina ganin ya ƙone baki ɗaya."
"Lokacin da matata ta tafi domin kiran yan sanda na tafi zuwa gareji na. Na leƙa ta taga, naga gidan Stan na ci da wuta, hayaƙi na fitowa daga ciki da tagogin gidan."

Bayan gudanar da bincike, wata majiya ta shaida wa ABC News cewa Sarah da Stanley sun yi wata soyayya mai matuƙar rikitarwa.

A wani labarin na daban kuma Uwar gida ta danna wa Mijinta wuka har lahira daga zuwa bankwana zai koma dakin Amarya

Tsagwaron kishin mata ya yi sanadin rasuwar wani Mai mata biyu yayin da yake yi wa Uwar gida bankwana zai koma dakin Amarya.

Rahoto ya nuna cewa Uwar gidan mai suna Atika ta daba wa mijinsu wuka har lahira a Mararaba dake jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel