Wata Mata ta halaka dan uwanta tsoho dan shekara 75, ta yi basaja cewa kashe kansa ya yi

Wata Mata ta halaka dan uwanta tsoho dan shekara 75, ta yi basaja cewa kashe kansa ya yi

  • Wata mata ta yi sanadin mutuwar ɗan uwanta na jini kuma tsoho ɗan shekara 75 a duniya bayan samun sabani tsakanin su
  • Matar ta yi kokarin rufe laifinta ta hanyar shirya cewa kashe kansa ya yi, amma binciken yan sanda ya bankado lamarin
  • Hukumar yan sandan Anambra ta ce zata gurfanar da ita gaban Kotu da zaran ta gama bincike

Anambra - Rundunar yan sanda a Anambra ta kama wata mata, Ozioma Orakwe, yar shekara 27 bisa zargin halaka ɗan uwanta tsoho ɗan shekara 75, Martin Orakwe.

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a Agulu, ƙaramar hukumar Anaocha, bayan sabani ya shiga tsakanin su har ta yi sanadin mutuwarsa.

Ana zargin cewa Ozioma Orakwe ta kashe tsohon mutumin kuma ta rataye shi domin jan hankalin mutane su ɗauka shi ne ya halaka kan shi.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi: Mutumin da aka Birne da rai ya bayyana a Hedkwatar yan sanda ta jiha

Hukumar yan sanda
Wata Mata ta halaka dan uwanta tsoho dan shekara 75, ta yi basaja cewa kashe kansa ya yi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar Laraba da ta gabata ne, rahoto ya karaɗe yankin Agulu cewa wani mutumi ya kashe kansa ba tare da barin dalilin aiwatar da haka ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane hali ake ciki a yanzun?

Kakakin yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a.

Ya ce tun farko hukumar yan sanda ta samu labarin, amma da ta tsananta bincike ta gano cewa kashe mutumin aka yi, aka shirya yadda kowa zai tsammanin kashe kansa ya yi.

A cewar kakakin yan sandan, kwamishinan jihar, CP Echeng Echeng, ya shawarci al'umma su rika neman hanyar sulhunta banbancin da ya shiga tsakanin su, mai makon faɗa da tada rikici.

Punch ta rahoto Mista Ikenga ya ce:

"CP ya ba da shawarin ne yayin da yake tsokaci kan wata mata da aka kama da zargin kashe tsoho ɗan shekara 75 a kauyen Amatutu, ƙaramar hukumar Agulu Anaocha.

Kara karanta wannan

Zamfara: Yan bindiga sun bude wa juna wuta a kasuwa, rayuka da dama sun salwanta

"Sabanin rahoton da muka samu da farko cewa kashe kansa ya yi, mun gano cewa mamacin na ɗauke da raunin makami a kansa, da tabon faɗa a jikinsa."
"Bayanan da muka samu bayan haka ya nuna cewa mamacin ya samu sabani da wacce ake zargi, hakan ya yi sanadin dambacewa tsakanin su.

Kakakin yan sanda ya kara da cewa Mamacin ya rasa rayuwarsa ne yayin faɗan da suka yi, amma domin kare kanta, shi ne ta haɗa basaja kamar kashe kansa ya yi.

Bugu da kari, yace sun samu bayanai masu amfani daga bakin wacce ake zargi, kuma za su gurfanar da ita a Kotu da zaran sun kammala bincike.

A wnai labarin kuma Mata ta kai karar Mijinta Kotu kan yana cusa mata tarkace a Al'aura idan suna saduwa

Wata mata ta maka Mijinta Uban ƴaƴanta a gaban Kotu bisa zargin yana cusa mata tarkace a al'aura yayin saduwar aure.

Kara karanta wannan

An tsinci gawar saurayi da Budurwa a cikin Mota, ana zargin suna saduwa suka mutu

Matar ta shaida wa alkalin Kotun a Abuja cewa ta ɗana masa tarko ta tabbatar da abin da yake mata, amma mijin ya musanta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel