Hankula sun tashi: Mutumin da aka Birne da rai ya bayyana a Hedkwatar yan sanda ta jiha

Hankula sun tashi: Mutumin da aka Birne da rai ya bayyana a Hedkwatar yan sanda ta jiha

  • Mutane sun shiga tashin hankali yayin da mutunin da suka samu labarin an binne shi ya bayyana a hedkwatar yan sanda ta jihar Anambra
  • Hukumar yan sanda ta ƙaryata labarin dake nuna an binne mutumin da ransa, kuma ta ja kunnen masu yaɗa shi
  • Kwamishinan yan sandan jihar ya ba da umarnin yin bincike kan ainihin abin da ya faru

Anambra - Wani ɗan jihar Anambra, Olisa Igbonwa, da ya fito daga garin Alor, karamar hukumar Ademili ta kudu, wanda aka yaɗa jita-jitar an binne shi da rai ya bayyana a Hedkwatar yan sanda dake Awka.

Igbonwa, wanda ɗan garin su Ministan kwadugo, Chris Ngige, ne ya kai kansa Ofishin yan sanda na jihar, ya sanar da cewa yana nan a raye, ba wanda ya binne shi.

Kara karanta wannan

Zamfara: Yan bindiga sun bude wa juna wuta a kasuwa, rayuka da dama sun salwanta

Punch ta rahoto cewa wani Bidiyo da akai ta yaɗawa a Intanet ya nuna cewa dattawan Alor jihar Anambra sun binne Igbonwa da ransa.

Taswirar jahar Anambra
Hankula sun tashi: Mutumin da aka Birne da rai ya bayyana a Hedkwatar yan sanda ta jiha Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bidiyon ya bayyana cewa manyan mutanen kauyen sun yi taro suka ɗauki matakin binne shi saboda ya naɗa kansa sarautar 'Ichie Ngene.'

Jita-Jitar da aka yaɗa ta yi ikirarin cewa mutanen ƙauyen sun sanya Igbonwa a cikin Akwati suka binne shi a yankin kauyen.

Shin dagaske hakan ta faru?

A wata sanarwa, kakakin yan sandan jihar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce ikirarin da aka yi a cikin bidiyon ƙarya ne kuma ya saɓa.

Sanarwan ta ce:

"An jawo hankalin mu kan wani Bidiyo da ake yaɗawa na cewa an binne Igbonwa da ransa a kauyen Alor, wanda dattawan kauyen suka yanke haka sabida ya naɗa kansa wata sarauta."

Kara karanta wannan

An tsinci gawar saurayi da Budurwa a cikin Mota, ana zargin suna saduwa suka mutu

"Bidiyon ƙarya ce kuma ya saba wa doka. Hukumar yan sanda na sanar da cewa Olisa Igbonwa, na nan da ransa kuma ba bu wanda ya binne shi."

Ina maganar mukamin sarautar ya kwana?

Bayan haka kakakin yan sandan ya ce hukumarsu ta karbi korafin cewa HRM Igwe Alor, ya naɗa Igbonwa wata sarauta amma ana masa barazanar ya aje rawanin cikin kwana 30.

"A halin yanzun kwamishinan yan sanda ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin domin gano haƙiƙanin abinda ya faru."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun halaka dandazon mutane

Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun aikata mummunar ɓarna a kauyen Amangwu Ohafia dake yankin jihar Abia .

Rahoto ya nuna cewa maharan sun halaka mutane ma su adaɗi mai yawa, wanda har yanzun ba'a gano yawan su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel