Yadda Aka Yi Rabon Biredi A Wajen Wani Kasaitaccen Biki Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Ja Hankali

Yadda Aka Yi Rabon Biredi A Wajen Wani Kasaitaccen Biki Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Ja Hankali

  • Wani bidiyo da ya yadu ya nuna yadda mahalarta taron biki suka cika da mamaki bayan an raba masu biredi
  • Yayin da kowannensu ke karban rabonsa na bikin, suna ta sake dubawa don ganin ko mafarki suke yi
  • Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun bayyana cewa rabon ya burge kuma za a ta maganar ma’auratan na shekaru da dama

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta wallafa bidiyon rabon da aka yi a wani bikin aure.

An shirya manya-manyan biredi a leda sannan aka rabawa kowani mutum da ya halarci taron. Mahalarta taron sun cika da mamaki a lokacin da suka karbi rabonsu suna ta al’ajabin abun da ke faruwa.

Shagalin biki
Yadda Aka Yi Rabon Biredi A Wajen Wani Kasaitaccen Biki Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Ja Hankali Hoto: TikTok/@ogtomisin
Asali: UGC

Akwai Hoton ma’auratan a jikin biredin da aka raba

Kara karanta wannan

APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

Matashiyar da ta wallafa bidiyon ta rubuta a jikinsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Abu daya game da mahaifina..yana nuna kai a kodayaushe.”

An kawo biredin ne kan farantai yayin da wani mutum ke ta rabawa mutanen wajen. Biredin na dauke da hoton amarya da ango a jikinsa.

Kalli bidiyon a kasa:

A daidai lokacin rubuto wannan rahoton, bidiyon ya tattara masu kallo fiye da miliyan daya da kuma ‘likes’ fiye da 200,000.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

Melissa ta ce:

“Zan kwashi Karin wasu a motata yayin da kowa ke cikin rudani.”

anjola ta ce:

“Wannan na iya zama kyautan biki mafi kyau da na gani.”

user9406834767828 ta ce:

“Duba wannan abu ne da mutum zai iya amfani da shi.”

Afi Atchale ta ce:

“Goggonin da kawunnan za su shafe shekaru suna magana kan wannan.”

Kara karanta wannan

Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu

Queenie Pooh ta ce:

“Shin wani zai iya yi mun bayanin amfanin wannan biredin?”

Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai suna Princess Mimi ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta koka kan cewa har yanzu bata auru ba duk da yawan shekarunta.

Matashiyar mai shekaru 38 ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta dungi sharban kuka a cikin wata mota yayin da take fallasa asirin zuciyarta.

Princess ta ce zata cika shekaru 39 a bana, kuma har yanzu bata yi aure ko mallakar da nata na kanta ba kuma bata da wani tsayayye da zai fito neman aurenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel