Baturiya mai auren ‘Dan Najeriya ta rangada ado, ta ci ankon atamfa da yara da mai gidanta

Baturiya mai auren ‘Dan Najeriya ta rangada ado, ta ci ankon atamfa da yara da mai gidanta

  • Wata mutumiyar kasar waje ta sa mutane su na ta surutu saboda wata irin shigar da ta rangada
  • Misis Nwanyi Ocha ta fito shafinta na Twitter ta wallafa hotonta dauke da atamfa tare da iyalinta
  • Ocha ta ziyarci kauyen surukanta inda aka yi jana’izar Sarkin garin Isuofia wanda ya rasu kwanaki

Wata mutumiyar kasar Switzeland da ke auren ‘dan Najeriya, ta dandasa gayun da ya jawo masu bibiyar kafofin sada zumunta suke ta magana.

Wannan Baiwar Allah da aka sani da Nwanyi Ocha, tayi shiga ne kamar asalin ‘yar Najeriya.

Kamar yadda Legit.ng ta kawo rahoto, Nwanyi Ocha ta dinka atamfa, ta sa zuwa wajen jana’izar Mai martaba Sarkin kasar Isuofia, Cif Agbazue.

Cif Agbazue shi ne yake sarautar kauyen Isuofia inda mai gidanta ya fito. Baturiyar da ke surukuntaka da Najeriya, ta halarci jana’izarsa.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Ko da ana alhinin rashin Basaraken ne, wannan bai hana mutanen kasar Isuofia cin gayu da yin biki na musamman yayin da aka birne Sarkin ba.

Nwanyi Ocha
Iyalin Nwanyi Ocha Hoto; Twitter/Nwanyi Ocha
Asali: Twitter

Da take magana a shafinta na Twitter, Ocha ta ce sun ci ado da kayan gargajiya a wajen makoki tare da mai gidanta da sauran 'ya 'yansu uku.

Nwanyi Ocha sun ci anko

“A rana ta biyu na jana’iza, mun canza kayan mu. Wannan karo mun sa atamfar da suke dauke da hoton Mai martaba.”
“Wannan hanya ce mai kyau da za a tuna da shi.”

Ganin atamfar jana’izar sun yi wa Ocha kyau a jiki, wata ‘yar uwarta Baturiya mai suna @keeng_hartor a shafin Twitter, tace abin ya ba ta sha’awa.

“Iyalinku sun burge ni, ina fatan in fara irin wannan da nufin sanin Afrika.”

Kara karanta wannan

Me yasa ka kashe ta: Mahaifiyar Haneefa da aka yiwa kisan gilla ta farmaki makashin 'yarta

Kwanan nan Nwanyi Ocha ta bayyana cewa ta bar Isuofia bayan an birne Mai martaba. Ocha tayi rubutu, ta bayyana yadda tayi kewar barin wannan gari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel