Shekaru 24 da faruwar lamari, Janar Abdussalam ya fadi yadda Abiola ya mutu a daure

Shekaru 24 da faruwar lamari, Janar Abdussalam ya fadi yadda Abiola ya mutu a daure

  • Tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ya bada labarin yadda MKO Abiola ya mutu
  • Cif MKO Abiola ya rasu ne a ranar 7 ga watan Yunin 1998 a lokacin yana tsare a hannun gwamnati
  • Abdussalami wanda yake mulki a 1998, ya ce rashin lafiya ya kama Abiola ne yana ganawa da Amurka

Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya yi hira ta musamman da gidan talabijin na Trust TV, inda ya karyata cewa guba ce ta kashe Mashood Abiola.

A cewar Abubakar, rashin lafiya ya kashe Abiola, akasin abin da ake fada cewa guba aka ba shi a tsare, shekaru biyar bayan ya yi takarar shugaban kasa.

Jaridar PM News da ta bibiyi hirar, ta rahoto Abdussalami yana cewa ya na dariya saboda akwai rade-radi nan-da-can cewa mu muka hallaka MKO Abiola.

Kara karanta wannan

Farfesan farko na Physics, Muhammad Sani Abubakar, ya riga mu gidan gaskiya

"A duk lokacin da nake magana a kan Marigayi Abiola, ina godewa Ubangiji da ya ba ni dabarar abin da zan yi a sa’ilin da ya bani shugabancin kasar nan.”
“A ranar da Moshood Abiola ya cika, Allah ya jikinsa, abubuwa biyu ko uku sun faru da suka sa na ke godewa Ubangiji da ya yi mani jagoranci.” - Abdussalami.

Haduwar Abiola da Amurka

Na farko, na karbi bakuncin tawaga daga kasar Amurka a karkashin jagorancin Pickering, a lokacin yana sakataren gwamnati ko makamancin haka.”

“A tawagar zan iya tunawa da kyau akwai Susan Rice. Zan tuna ta sosai saboda rawar da taka daga baya.”
“Bayan mun gama tattaunawa za su bar ofishina, sai Pickering ya ce mani “’Yallabai mun nemi mu ga Mashood Abiola, amma an hana mu.’”

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ba zan bari wani ya hada 'yan daba su dauki makami ba, inji Buhari

Na ce: ‘Meyasa aka hana ku? Wanene ya hana ku?’ Nan take na dauki mataki, na ce za ku gana da Abiola, Na fadawa CSO cewa ya hada su da Abiola.

Allah ya sa a gaban wasu aka yi

Tsohon shugaban ya ce da farko babu mai ganin Abiola sai likitansa, amma da ya karbi mulki sai ya bada dama ‘yanuwansa su samu damar ganin shi a tsare.

Ana irin wannan yanayi da ‘yanuwansa suke ganawa da shi ne sai tawagar Amurkan ta je ta hadu da Abiola, a nan kwatsam sai rashin lafiya ya kama shi.

“A wajen wannan zama da tawagar Amurka sai Abiola ya fara rashin lafiya, nan-take da jami’an tsaro suka kira Likitoci su duba shi, sai aka zarce asibiti.”
“Abin bakin-ciki, a asibitin ya rasu. CSO dina ya kira ni, ya fada mani cewa yana da labarin bakin-ciki; ya ce Abiola ya mutu. Abin ya yi matukar girgiza ni."

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

Ya za mu fadawa dangin Abiola?

Matsalar bayan nan ita ce yadda za a sanar da iyalin marigayin ya mutu, Abdussalami ya ce Babagana Kingibe ya taimaka wajen tattaro iyalin Abiola.

Janar Abdussalami ya ce ya shiga ba danginsa hakuri, har Susan Rice ta ce wannan ba aikinsa ba ne, ta shiga lallashin su kafin a sanar da mutuwar ga Duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel