Hotuna: Labarin dattijon da ya kirkiri gidan radiyo, jirgi da risho mai amfani da ruwa

Hotuna: Labarin dattijon da ya kirkiri gidan radiyo, jirgi da risho mai amfani da ruwa

  • Ganawar Legit.ng Hausa da wani dattijo ta zakulo bayanai masu ban mamaki da 'yan Afrika kan iya yi
  • Malam Hadi Usman, wani dattijo a jihar Gombe ya ce shi ya fara kirkirar gidan radiyo mai zaman kansa a jihar Kano
  • Ya kuma bayyana yadda ya kirkiri wata na'ura mai iya sarrafa komai da ke alaka da wuta a gidansa da dai sauran ayyuka sama da 40

Jihar Gombe - Wani dattijo mai suna Malam Muhammad Hadi Usman ya yi fice wajen kirkirar abubuwan ban mamaki na fasaha tun yana matashi.

A hirar da yayi da Legit.ng Hausa, dattijon ya bayyana yadda ya kirkiri tashar radiyo mai zaman kanta a gidansa, kafin daga bisani ya mai she ta zuwa jihar Kano.

Kara karanta wannan

Na musamman: Fasihin dattijo ya kirkiri risho mai amfani da ruwa maimakon gas ko kalanzir

Idan baku manta ba, a baya Legit.ng Hausa ta rahoto Malam Hadi yana bayyana yadda ya kirkiri jirgi mai saukar ungulu, kana a baya-bayan nan ya kirkiri risho mai amfani da ruwa.

Malam Hadi Usman mai abun mamaki
Ban taba shiga aji ba: Dattijo ya ce shi ya kirkiri gidan radiyo mai zaman kansa a Kano
Asali: Original

A wani sashen hirar, ya shaida wa wakilinmu cewa, shi ne mutum na farko da ya fara kirkirar gidan radiyo mai zaman kansa a jihar Kano, inda ya nuna shaida daga jaridar Weekend Triumph da ta wallafa labarinsa a ranar 25 ga watan Janairun 1992.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, ya bayyana yadda yayi gwagwarmayar yawo domin koyar da al'umma da basu ilimin da yake dashi, inda ya zaga jihohin Adamawa, Borno, Kano da ma kasashen ketare.

Ya kuma ce, ya fara

Da yake karin haske kan kirkirar gidan radiyo mai zaman kansa a Kano, Malam Hadi ya ce:

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

"Lokacin da naje Kano, Kano ta yi girma. Wa ya sanni? wa zai san nazo? Sai nayi amfani da waccar dama. A Gombe tun 1977 aka fara nuna gidan radiyo na. Saboda sai nayi babban gidan radiyo a Kano.
"Sai na tallata shago na, da nayi tallan shago na a cikin sati daya aiki ya taro yayi yawa. Sai Weekend Triump ta zo tayi hira dani, na zama nine na farko na fara yin gidan radiyo mai zaman kansa a Kano. A lokacin gwamnati taba ba da damar yin gidan radiyo mai zaman kansa ba.
"Kuma abin mamaki, ba a turo wata hukuma tazo ta tuhume ni ko a kama ni cewa na kaifi ba."

Da wakilinmu da ya tambaye shi ko ya taba karatun ilimin zamani na kimiyya da fasaha mai zurfi, Malam Hadi ya ce bai taba shiga aji ba, kawai dai bincike yake da kuma zama da kwararru a bangaren da yake da sha'awa a kai.

Kara karanta wannan

KAROTO ga 'yan daidaita sahun da suka shiga yajin aiki: Za ku gane shayi ruwa ne

"Na taba karantarwa a jami'a har guda biyu a kan fannin kayan wuta, amma ni da kaina a gaskiya ko leka ban taba yi ba da sunan neman ilimi."

Kalli jaridun da suka wallafa labarinsa a shekarun baya:

Malam Hadi Usman mai ban mamaki
Ban taba shiga aji ba: Dattijo ya ce shi ya kirkiri gidan radiyo mai zaman kansa a Kano
Asali: Depositphotos

Malam Hadi Usman mai abun mamaki
Ban taba shiga aji ba: Dattijo ya ce shi ya kirkiri gidan radiyo mai zaman kansa a Kano
Asali: Depositphotos

Malam Hadi Usman mai abun mamaki
Ban taba shiga aji ba: Dattijo ya ce shi ya kirkiri gidan radiyo mai zaman kansa a Kano
Asali: Depositphotos

Malam Hadi Usman mai abun mamaki
Ban taba shiga aji ba: Dattijo ya ce shi ya kirkiri gidan radiyo mai zaman kansa a Kano
Asali: Depositphotos

Na kirkiri na'urar da zan iya sarrafa komai na gidana a kan gado na

Malam Hadi ya kuma shaida cewa, ya kirkiri wata na'ura a gidansa, wacce ke kula da duk wasu abubuwan da ke faruwa a gidan, kama daga wutar lantarki, talabijin, radiyo, yanayi, da dai sauran abubuwan da gidan ke kunshe dashi.

A cewarsa, na'urar da ya nuna wa wakilinmu tana amfani sama da 40, inda ya nuna yadda ake amfani da ita dalla-dalla.

Ya kuma yi nuni da yadda ya fuskanci kalubalen masu satar fasaharsa, inda yace ya sha zuwa kasuwa sai ya ga an kwafe wata fasahar da ya kirkira.

Sai dai, domin samo mafita, Malam Hadi ya ce ya shafe watanni yana bincike, inda ya samo makullin da zai ke dakile wannan matsala ta satar fasaha.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Da aka tambaye shi ko ya taba fuskantar kalubale daga gwamnati ko wata kungiya, ya ce bai taba ba, sai dai abin takaici babu wata gwamnati da ta taba taimakonsa; karamar hukuma, jiha ko tarayya.

A bangarensa, ya ce bai gajiya duk da yawan shekarunsa, kofarsa a bude take ya koyar da duk mai bukatar koyon sana'arsa.

Tare da irin wadannan mutanen, mutane da dama sun yi imanin cewa, kasar nan tana da hazikan da za su ciyar da ita gaba.

Na'urar malam Hadi
Na'urar da ke ayyuka sama da 40 da Malam Hadi ya kirkira
Asali: Original

A wani rahoton kunji cewa, yayin da ake tsananin bukatar mafita ga tsadar rayuwa a Najeriya, wani dattijo ya jima da samar da sauki a wani bangaren; ta hanyar samar da risho din girki mai amfani da ruwa.

Makwanni kadan da suka gabata ne kafafen sada zumunta suka cika da ta'ajibi ganin wani dattijo yana amfani da ruwa wajen samar da makamashi.

Wannan yasa, Legit.ng Hausa tayi tattaki zuwa inda wannan dattijo yake a jihar Gombe domin jin ta bakinsa da kuma tsare-tsaren da yake yi a nan gaba.

Kara karanta wannan

Yadda magidanci ya kashe matarsa da duka bayan sun samu sabani a Nasarawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel