Matar Aure ta garzaya kotun musulunci, ta nemi mijinta ya sake ta kuma ya bata kudin abinci na shekara 2

Matar Aure ta garzaya kotun musulunci, ta nemi mijinta ya sake ta kuma ya bata kudin abinci na shekara 2

  • Wata matar aure, Fulera Lawal, dake zaune a yankin Doka na garin Kaduna ta gurfanar da mijinta a gaban kotun shari'ar musulunci
  • Matar ta nemi kotun ta raba auren su, kuma ta umarci mijin ya bata kudin ciyarwa na shekara biyu, sannan ya dauki nauyin ɗansa
  • A cewar Fulera, mijin ya bar ta a gidan iyayen ta tun shekarar 2020, kuma iyayen ta ne suka cigaba da ɗaukar nauyin ta da ɗan su

Kaduna - Wata matar aure yar kimanin shekara 30 a duniya, Fulera Lawal, a ranar Laraba, ta gurfanar da mijinta gaban kotun shari'ar musulunci dake Magajin Gari, jihar Kaduna.

A rahoton Daily Trust, matar ta nemi kotun ta raba aurenta da mai gidan ta, Kabir Abdulhamid, kuma ta umarce shi ya biya ta kudin ciyarwa na shekara biyu.

Kotun musulunci
Matar Aure ta garzaya kotun musulunci, ta nemi mijinta ya sake ta kuma ya bata kudin abinci na shekara 2 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Fulera, wacce ke zaune a yankin Doka ta Kaduna, ta shaida wa kotun cewa mijin ya bar ta a gidan iyayenta tun shekarar 2020.

A cewarta, tun wancan lokaci iyayen ta ne ke kokarin ciyar da ita da kuma ɗan da suka haifa da mijinta, Kabir Abdulhamid.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kazalika, Malama Fulera ta kuma nemi kotun ta umarci mai gidan nata daga yanzun ya ɗauki cikakken nauyin kulawa da ɗan da ta haifa masa.

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Bayan sauraron korafin matar, alkalin kotun mai shari'a, Murtala Nasir, ya umarci Fulera Lawal ta lissafa adadin kudin da ta kashe wajen ciyarwa na tsawon shekara biyu kamar yadda ta bukata.

Daga nan kuma sai alkalin ya sanar da ɗage sauraron karar har zuwa ranar 19 ga watan Janairu, na asabuwar shekaran da muka shiga, 2022.

A wani labarin na daban kuma Wani mutumi ya yi lalata da mata 10 a Otal da sunan Kwamishinan jiha

Yan sanda sun yi ram da wani mutumi bisa zargin amfani da sunan kwamishinan Akwa Ibom yana damfaran mutane.

Kakakin yan sanda na jihar, Odiko Macdon, yace wanda ake zargi ya kwanta da mata 10 bisa alkawarin zai taimaka musu su samu aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel