Hotunan kyakkyawar ɗiyar gwamnan Arewa da masoyinta abokin rayuwa

Hotunan kyakkyawar ɗiyar gwamnan Arewa da masoyinta abokin rayuwa

  • A watan Yuli da ya gabata cikin wannan shekarar, 2021, aka ɗaura auren diyar gwamnan Bauchi, Zara Bala Muhammed
  • Sai dai bikin wanda kusan za'a ce ba'a gudanar da wasu shagulgula ba, amma yanzun ma'auratan na shirin nuna farin cikin su
  • Mun tattaro muku wasu kyawawan hotunan masoyan biyu yayin da suke shirin gudanar da shagalin auren su

Bauchi - Fatima Zara, ɗiyar gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi, tare da masoyinta kuma abokin rayuwarta (wato mijinta), Masha Sheriff, sun saki sabbin hotuna.

Rahoto ya bayyana cewa tun a watan Yuli na wannan shekarar da muke ciki aka ɗaura auren Zara da angonta Masha, ba tare da gudanar da manyan shagulgula ba.

Gidauniya TV ce ta tura waɗan nan hotunan a shafinta na dandalin sada zumunta Facebook.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Kashe Fitaccen 'Dan Kasuwan Najeriya a Afirka ta Kudu

Sai dai ga dukkan alamu masoyan biyu da suka zama ɗaya, sun fara shirye-shiryen faɗaɗa shagulgulan bikin auren su.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin kyawawan hotunan ma'auratan yayin da suke shirin shagalin aure.

Hotunan da suka fitar kwanan nan

Zara da Masha
Hotunan kyakkyawar ɗiyar gwamnan Arewa da masoyinta abokin rayuwa Hoto: Gidauniya TV
Asali: Facebook

Zara da Masha
Hotunan kyakkyawar ɗiyar gwamnan Arewa da masoyinta abokin rayuwa Hoto: @Gidauniya TV
Asali: Facebook

Zara da Masha
Hotunan kyakkyawar ɗiyar gwamnan Arewa da masoyinta abokin rayuwa Hoto: Gidauniya TV
Asali: Facebook

Zara da Masha
Hotunan kyakkyawar ɗiyar gwamnan Arewa da masoyinta abokin rayuwa Hoto: Gidauniya TV
Asali: Facebook

Zara Bauchi
Hotunan kyakkyawar ɗiyar gwamnan Arewa da masoyinta abokin rayuwa Hoto: @Gidauniya TV
Asali: Facebook

Zafafan Hotunan Jaruma Rahama Sadau

A wani labarin na daban kuma, mun atattaro muku Sabbin zafafan Hotunan Jaruma Rahama Sadau a wurin daukar fim a Bollywood na ƙasar Indiya

Tun a baya dai Sadau ta saka hotuna a dandalinta na sada zumunta, inda tace tana aikin shirin fim da masana'antar Bollywood.

Rahama Sadau, ta saba jawo cece kuce kan shigar da bata dace da addininta ba kuma ta dora a kafar sada zumunta.

Kara karanta wannan

Abinda Shugaba Buhari ke yi kullum don kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

Rahama Sadau ta cigaba da tura zafafan hotunanta tare da wasu jaruman masana'antar shirya fina-finan India, yayin ɗaukar shirin fim ɗin da aka raɗa wa #KhudaHafeezChapter2.

Asali: Legit.ng

Online view pixel