Femi Fani-Kayode ya maidawa tsohuwar matarsa martani bayan tace shi ragon namiji ne

Femi Fani-Kayode ya maidawa tsohuwar matarsa martani bayan tace shi ragon namiji ne

  • Femi Fani-Kayode ya zargi tsohuwar mai dakinsa, Precious Chikwendu da fama da cutar kwakwalwa
  • Lauyan tsohon Ministan ya fitar da jawabi, inda ya yi wa Chikwendu raddi a kan abin da ta fada kwanaki
  • A baya aka ji bazawarar ta na cewa ba ta taba samun wata alaka da Cif Fani-Kayode ba domin bai da lafiya

Tsohon Ministan harkokin jirgin sama, Femi Fani-Kayode, yace uwar ‘ya ‘yansa hudu, Precious Chikwendu ta na fama da larurar ciwon kwakwalwa.

Jaridar Premium Times ta ce Femi Fani-Kayode ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar ta bakin wani lauyansa, Ayodeji Ibikunle a ranar Alhamis.

A cewar Fani-Kayode tsohuwar mai dakinsa, Chikwendu ta na da wata cuta da ke sa halin da mutum yake ci ya rika juyawa daga lokaci bayan lokaci.

Kara karanta wannan

Dala daya (N409.89) na biya kudin sadaki, Matashin da ya auri yar shekara 70

Haka zalika tsohon Ministan yace wannan Baiwar Allah ta na dauke da cutar da ake kira ‘schizophrenia’, wanda take hana mutum tunani da kyau.

Precious Chikwendu ba ta da lafiya - FFK

“Ya zama dole mu bayyana cewa Miss Precious Chikwendu, tsohuwar abokiyar zaman wanda mu ke karewa, Cif Femi Fani-Kayode, Sadaukin Shinkafi, ta na da cututtukan 'bipolar disorder and schizophrenia', mun kuma yarda cewa sam ba ta da hankali.” - Lauya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Femi Fani-Kayode
Femi Fani Kayode da Precious Chikwendu Hoto: www.naijanews.com
Asali: Facebook

Lauyan yace ana zaune kalau, bai kamata su biyewa munanan zargin da Chikwendu tayi ba, domin abin da ta fada cike su ke da kazanta da rashin daraja.

Ibikunle ya kuma musanya zargin Miss Chikwendu na cewa daya daga cikin ‘ya ‘yanta da Fani-Kayode ya kamu da cutar COVID-19 ko ya samu ciwo a kansa.

Lauyan da ya tsayawa ‘dan siyasar yace abubuwan da Precious Chikwendu take fada zuki-ta-malle ne. Jaridar nan ta This Day ta fitar da irin wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Hare-hare sun yawaita a Zamfara, tawaga ta tafi ganawa da kasurgumin dan bindiga

Precious Chikwendu tayi magana

Chikwendu ta maida martani, inda ta zargi lauyan na Fani-Kayode da mangare ta a kotu. Bazawarar tace har yanzu wannan mutumi bai nemi afuwarta ba.

Precious Chikwendu tace lafiyar ta lau, sai dai idan tsohon mijinta ne yake da tabin kwakwalwa. Chikwendu tayi magana a Twitter, tace za ta fito da hujjoji baro-baro.

Ban taba kwanciyar aure da shi ba

Ita dai wannan Baiwar Allah da ta haifawa ‘dan siyasar ‘ya ‘ya hudu ta ce ba su taba samun wata mu’amala ba har ta bar gidansa saboda bai da isasshiyar lafiya.

Sarauniyar kyawun ta zargi 'dan siyasar da cin zarafinta sau da yawa a lokacin da suke tare, sannan tace ya umarci masu gadinsa da su garkame ta a gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel