An saki hotunan fursunoni fiye da 250 da suka tsere a gidan yari, ana neman su ruwa a jallo

An saki hotunan fursunoni fiye da 250 da suka tsere a gidan yari, ana neman su ruwa a jallo

  • Ma’aikatar harkokin cikin gida ta bada sanarwa game da wadanda suka fice daga kurkukun Jos
  • Gwamnatin tarayya ta na neman mutane sama da 250 da suka tsere daga gidan yari a makon jiya
  • An sa lada ga duk wanda ya iya taimakawa da bayanin yadda za a sake cafke mutanen da suka tsere

Abuja - Ma’aikatar harkokin cikin gidan Najeriya ta fitar da hotunan wasu daga cikin mutanen da suka tsere daga gidan yarin garin Jos a karshen makon jiya.

Akalla mutane 262 suka tsere daga kurkuku ranar Lahadi, 28 ga watan Nuwamba, 2021, a jihar Filato. A halin yanzu gwamnati na cigiyar wadannan mutane.

Hukumomi sun yi nasarar sake damke mutane goma, amma sama da mutum 250 sun yi dabo.

A ranar Alhamis, 2 ga watan Disamba, 2021, ma’aikatar cikin gidan ta yada hotunan ragowar ‘yan gidan yarin 252 da yanzu sun sulale, an rasa inda suka shiga.

Kara karanta wannan

Wadanda suka tsere daga gidan yarin Kogi ne ke da alhakin kai hari Masallacin Neja, 'Yan sanda

Ma’aikatar tarayyar ta ba al’umma shawarar su garzaya zuwa ofishin ‘yan sanda da zarar sun ci karo da ko da daya daga cikin wadannan mutane da ake nema.

Ma’aikatar ta ja-kunnen jama’a cewa wadannan Bayin Allah da ake nema ruwa-a-jallo, su na da hadari. Jaridar Premium Times ce ta fitar da wannan rahoto dazu.

Hotunan fursunoni
Fursononin da suka tsere Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sanarwar da ta fito daga bakin NCoS

“Wadannan mutane da ke sama sun tserewa kaso daga gidan gyaran hali da ke garin Jos a ranar Lahadi, 28 ga watan Nuwamba, 2021.”
“A kira lambar sauraron koke na gidan gyaran hali na Najeriya, NCoS ta layin 09060004598, 08075050006 domin bada shawara, ko idan an yi ido-biyu, ko za a bada wani bayani game da inda aka gansu.”
“Kyauta ta na jiran duk wanda ya kawo wani bayani mai muhimmanci.” – NCoS.

Kara karanta wannan

Omicron: Abin da ya dace a sani kan sabon samfurin COVID-19 da ke neman sake rufe kasashe

Baya ga alkawarin tukuwici, ma’aikatar tarayyar ta kuma ja-kunnen jama’a da cewa babban laifi ne a doka, a taimakawa duk wanda ya tsere daga gidan kurkuku.

Ballewa daga gidan yari ya fara yawa

A cikin shekara daya, an yi yunkurin balla gidan yari sau 15 a Najeriya, kuma masu wannan danyen aiki sun yi nasarar tserewa da ‘yan zaman kaso sau takwas.

Ku na da labari cewa akalla mutane 11 suka mutu, yayin da daruruwan fursunoni suka tsere daga gidan gyaran hali da ke jihar Filato bayan abin da ya faru a makon jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel