Martanin mutane kan wani saurayi da ya kori budurwa saboda ba tayi kama da hotunan Istagram ba

Martanin mutane kan wani saurayi da ya kori budurwa saboda ba tayi kama da hotunan Istagram ba

  • Wani saurayi da ya gaza hakuri ya umarci budurwarsa ta fice daga ɗakinsa saboda ba ta yi kama hotunanta na Instagram ba
  • Rahoto ya tabbatar da cewa ya nuna sha'awarsa akan yarinyar ne bayan yaga hotunan ta a Instagram, amma abin ba haka yake ba a fili
  • A wani gajeren bidioyo da ya tura, mutumin ya nuna rashin jin daɗinsa kan banbancin da aka samu, amma budurwar ta nuna ba haka bane

Soyayyar wasu masu amfani da kafar sada zumunta ta rushe tun kafin a fara bayan saurayin ya kori budurwar daga ɗakinsa a haɗuwar farko.

Mutumin ya sallami matar daga ɗakin ne saboda ganin ta ba tare da wasu abubuwa da ya saba gani a hotunanta na Instagram ba.

A wani gajeren bidiyo da Thetattleroomng suka buga a Instagram, mutumin ya kwatanta hotunanta na kafar sada zumunta da kuma yadda take a zahiri.

Kara karanta wannan

Shi kaɗai ya san inda na ke ajiye asusun: Budurwa ta faɗa wa kotu saurayin ta ne ya sace mata kuɗi

Saurayi da budurwa
Mutane sun maida martani kan wani Saurayi da ya kori budurwarsa saboda ba tayi kama da Hotonta ba Hoto: @thetattleroomng
Asali: Instagram

Ko me budurwan tace wa mutumin?

A kokarin kare kanta, budurwan wacce ta amince da laifinta, ta yi wa mutumin bayanin cewa girman bayanta a haka ma ai ya yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin bai gamsu da bayananta ba, hakan yasa ya mika mata dala $400 (N164,560) kuma ya umarci ta fice masa daga ɗaki.

Mutane sun maida masa martani

@gracechristopher7 ya rubuta cewa:

"Meyasa mutumin bai haɗa da kansa ba a bidiyon? Nasan ya fi yarinyar muni, da ce mata ya yi ta tafi kawai maimakon ya ɗauki bidiyonta."

@opw_popstore tace:

"Ba ta yi asara ba, idan nice zan kama gaba na ne, na samu dala $400 a kyauta. Mu irin wannan mazajen muke so, su biya kuma su sallame mu."

@Zeepet_ ta bayyana ra'ayinta da cewa:

"Wannan mutumin ya so kunyata ta ne kawai, duk da tana da ƙiba amma kyakkyawa ce. Irin wannan ne yake sa suje a saka musu abinda basu da shi."

Kara karanta wannan

Budurwa ta fasa kwalba ta caka wa direban motar haya saboda kudin mota a Legas

@mabelthegoddess yace:

"Dan tsaya daga karshen bidiyon nan, ba shi na ji yana cewa na ji daɗin haɗuwa dake ba sanda zata fita? Me kuma yake bukata daga baya."

A wani labarin kuma Yan Najeriya sun yi martani kan wani matashi da ya ci F9 a darussan NECO, Ya kammala digiri da darajar farko

Wani matashi ya nuna farin cikinsa da kammala digiri bayan ya ci F9 a darussan NECO da ya zauna karon farko.

Mayowa Joshua Amusan ba shi kaɗai ya kammala digiri da sakamako mai daraja ta farko a jami'ar Ibadan ba amma shine dalibi mafi hazaka a sashinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel