Wani magini mai fasaha ya dankara gida ta bai-bai, ya fito da bidiyon cikin wannan gida

Wani magini mai fasaha ya dankara gida ta bai-bai, ya fito da bidiyon cikin wannan gida

  • Wani hazikin mutumi mai suna Marek Cyran ya gina wani irin gida da samansa yake kallon kasa
  • Mista Marek Cyran ya gina wannan gida da ya ba kowa mamaki ne a yankin Niagara, kasar Amurka
  • Wannan mutumi yace ya samu basirar dandasa irin wannan gida ne bayan ya ziyarci kasar Foland

Niagara - Hausawa su na cewa hikima kashin kwance, wanda bai iya ba ya bata jikinsa. Wannan shi ne abin da Marek Cyran ya yi a yankin Niagara a kasar Amurka.

Legit.ng ta samu labarin Mista Marek Cyran wanda ya gina wani irin gida ta bai-bai. Saman wannan gida yana kallon kasa, yayin da kasan na sa ke kallon sama.

A lokacin da Cyran ya zo da wannan gini a shekarun baya, wasu sun ta yi masa dariya da izgili. Jaridar nan ta TuKo ta tabbatar da wannan labari a ranar Litinin dinnan.

Read also

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zaman don kallon jiragen kasa

A karshe kuwa ya ba marada kunya a cikin shekarar 2012, ya gina wannan gida da kusan babu wanda ya taba ganin irinsa a gangaren da ke yankin kudancin Ontario.

Gidan da yake a bai-bai

Komai na wannan gida a bai-bai yake, kamar yadda aka ambata saman rufin gidan ne a kasa, yayin da kasan gidan ya tashi sama, akasin abin da aka saba gani.

Wannan gida
Gida ta bai-bai Hoto: www.pinterest.de
Source: UGC

Komai na wannan gida a birkice yake kamar yadda bidiyon cikin gidan da Kool Buildings suka dauka ya nuna. An wallafa bidiyon duk dakunan gidan a Youtube.

Wurin dafa abinci da wurin zaman cin abinci da dakunan gidan duk a birkice su ke. Har wani shuka da aka yi a wannan gida mai hawa daya, duk a bai-bai yake.

Read also

Bidiyon budurwar da ta kashe N657k don yin karin gashi mai jan kasa ya janyo cece-kuce

Ana zuwa yawon bude ido

A halin yanzu wannan gida da Marek ya gina ya zama abin gani-da-kai, inda mutane daga wurare masu nisa suke zuwa Niagara domin su ga wannan abin mamaki.

Mutane su kan biya Dalolin kudi domin su ji yadda ake ji idan aka shiga cikin wannan gida da yake a bai-bai. Watakila jiri zai iya kama mutum da zarar ya shiga gidan.

Niagara, garin da wannan gida ya ke, yana kan iyaka ne tsakanin kasar Amurka da Kanada.

Mai fasaha ya kere mota mai kamar jirgi

A 'yan kwanakin bayan nan ne aka ji cewa wani Bawan Allah mai suna John, mai ‘dan karen hikima da fasaha, ya kirkiri wata mota mai tattare da gida a cikin ta.

Wannan motar tana zama iya kwale-kwale da zarar an tsunbula ta a cikin ruwa. A cikin wannan mota mai kamar jirgi, akwai gidan rawa ga masu bukatar cashewa.

Read also

Mai fasaha ya kera mota mai zama jirgi, cikinta kamar katafaren otel, har da gidan rawa

Source: Legit

Online view pixel