Latest
Mummunar gobara ta kashe dabbobi 78 a Danzago, jihar Kano. Hukumar kashe gobara ta ceto dabbobi da kayan amfani, yayin da jami’inta daya ya ji rauni a kafa.
Dakatar da ayyukan USAID ya kawo cikas ga rarraba kayan tazarar haihuwa a Bauchi, amma gwamnatin jihar ta ware N50m don tallafawa UNFPA wajen samar da kayayyakin.
Abba Kabir Yusuf ya ziyarci Rimin Zakara bayan rusau. Zai dauki nauyin wadanda suka rasu, za a gina masallacin Jumu'a, asibiti, titi da sauran ayyukan raya kasa.
Malaman Ebonyi sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani bayan wasu shugabannin kananan hukumomi sun gaza biyan albashin watanni uku na malaman firamare.
Fitaccen jarumin Nollywood wanda ke koyarwa a jami'ar Port Harcourt, Columbus Irisoanga da aka sani da taka rawar boka a fina-finai, ya riga mu gidan gaskiya
Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke JSS da SSS, ta kuma gabatar da tsarin karatun bai daya na shekaru 12 wanda zai taimaka wajen inganta ilimi a Najeriya.
Marcelo ya sanar da ritayarsa daga kwallon kafa bayan shekaru 16 a Real Madrid, inda ya lashe Champions League 5 da La Liga sau 6. Ya bugawa Brazil wasanni 58.
Bayan zargin shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani kan girke Lakurawa domin kawo cikas a mulkinsa, Majalisar Dattawa za ta yi bincike domin gano gaskiya.
Manjo Janar Chris Jemitola, tsohon mai tsaron lafiyar Olusegun Obasanjo, ya rasu bayan ya yanke jiki ya fadi a Abuja. Iyalinsa ba su sanar da lokacin jana’izarsa ba.
Masu zafi
Samu kari