Latest
Kungiyar JOD mai goyon bayan Bola Tinubu ta ce 'yan adawa masu shirin haduwa domin yakar Tinubu ba za su yi nasara ba. JOD ta ce 'yan APC na adawa da Tinubu.
Miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wani limamin addinin Kirista a jihar Rivers. 'Yan bindigan sun yi garkuwa da shi tare da wasu mutum biyu.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Gombe sun samu nasarar cafke wasu mambobin kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram. An cafke su ne a cikin wani otal.
Wasu al'ummar yankin Ipetumodu a jihar Osun sun shiga damuwa kan rashin sanin halin da sarkinsu, Oba Joseph Olugbenga Oloyede ke ciki tsawon lokaci.
Sanata Barau Jibrin ya yi ta'azziyar mutanen da tirela ta kashe a jihar Kano. Tirela ta murkushe mutane 23 har lahira inda mutuwar ta girgiza mutane a jihar Kano.
Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen, ya nada Alan Waka babban mataimaki. Masoya sun taya shi murna, suna addu’a Allah ya ba shi ikon sauke nauyi.
Jami'an tsaro na ƴan sanda da ƴan banga sun samu gagarumar nasara kan ƴan bindiga a jihar Kebbi. Sun kashe wasu daga cikinsu tare da ceto mutumin da suka sace.
Dr Usman Bugaje ya ce mulkin shugaba Buhari da Bola Tinubu bai tsinana komai ga Najeriya ba. Ya ce APC ta zamo annoba ga Najeriya wajen gaza gyara kasa.
Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da Samha M. Inuwa da Soja Boy bisa laifin tsiraici da batsa a bidiyo, tare da kwace lasisinsu. Mun yi bayani kan jaruman.
Masu zafi
Samu kari